Operation Hadarin Daji sun kashe ‘Yan bindiga 35, sun karbo shanu 24

A ranar Lahadi, 17 ga watan Junairu, 2021, rundunar sojojin Operation Hadarin Daji suka kashe ‘yan bindiga 35 a jihar Zamfara inji jaridar Punch.

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin kasar sun yi nasarar karbe wasu dabbobi da miyagun suka sace.

Babban jami’in yada labarai na hedikwatar tsaro ta kasa, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar a Gusau, jihar Zamfara.

John Enenche yace: “Bayan samun bayanai sport da sawun ‘yan bindiga dauke da dabbobin sata a Bungudu, jihar Zamfara, sojojin da ke Kekuwuje sun yi wuf, sun auka masu.”

Operation Hadarin Daji sun kashe ‘Yan bindiga 35, sun karbo shanu 24

“A wajen wannan arba, an hallaka ‘yan bindiga 30, yayin da aka karbo shanu 24, da tarin tumaki.”

Jami’in ya kara da cewa: “Haka zalika duka a wannan rana (17 ga watan Junairu), sojojin da ke Maradun sun samu labarin harin da aka sake kai wa a Janbako, Zamfara.”

An kama wani magidanci da kullum sai yayi zina da ‘yar cikinsa sau 3 yake jin dadi

“Dakaru sunyi maza-maza su kai farmaki domin dakile harin. An yi masu kwantan bauna daf da dajin Janbako inda aka gwabza.” Inji Manjo Janar John Enenche

“Dakarun sojoji sun sha karfin miyagun, suka hallaka biyar daga cikinsu. Yanzu haka ana neman ragowar wadanda suka tsere.”

Sojoji sun kuma yi nasarar damke wasu mutane biyu da ke hada-kai da ‘yan bindigan Zamfara.

Janar John Enenche a madadin sojojin Najeriya, ya tabbatar da cewa dakaru za su cigaba da lallasa masu tada kafar-baya da sauran makiyan kasa, har sai an sau zaman lafiya.

A baya kun ji cewa ‘yan sanda sun cafke wasu da ake zargi da laifin tada tarzoma a jihar Zamfara. Lamarin da har ya kai ga jawo asara a fadar Sarkin Shinkafi.

Rahotanni sun ce wannan jawabi na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu ya fitar a Gusau.

Wasu tsageru dauke da bindigogi da adduna da sanduna sun kai wa fadar Sarkin Shinkafi hari.

 546 total views,  8 views today

About M. Jamiu 1373 Articles
Muhammed Jamiu is a Head Editor at Mobilized9ja (M9JA). He has been publishing for 8 years and focused more on Local/World News, Nigeria Music & Video all in English and Hausa Language.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*