NURTW Ta Gargadi Direbobi Game Da Tukin Dare A Jihar Zamfara

0
72

NURTW Ta Gargadi Direbobi Game Da Tukin Dare A Jihar Zamfara

Kungiyar Direbobi ta Jihar Zamfara, watau N U R T W, karkashin jagorancin shugabanta na jihar, Alhaji Hamisu Kasuwar Daji, inda  ya gargadi direbobin da ke zirga-zirga a fadin kasar nan da su guji tafiyar dare.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a shelkwatar kungiyar ta jiha da ke Gusau babban birnin Jihar Zamfara.

Alhaji Hamisu Kaduwar Daji, ya kara da cewa, yanzu kasar nan ta shiga wani hali na matsalar Tsaro, hanyoyinmu photo voltaic zamo tarkon mutuwa da kuma masu neman kudin fansa. ‘Yan bindiga photo voltaic addabe mu ta kowane hali, don yanzu haka sakamakon matsalar su mun yi asarar rayukan Direbobi da dama a Zamfara kuma yanzu haka mutun uku na hannun maharan a Zamfara.

“Kuma wadannan ‘yan ta’adda suna cin karensu ba babaka ne da zarar duhu ya kama gab da magariba zuwa dare, don haka muke jan kunnan direbobinmu da su daina tafiyar dare, abin da Allah ya basu da rana su yi fatan Allah ya sa masa albarka. Saboda direbobinmu da aka kashe da wadanda ke hannun yanzu duk da dadare ne maharan suka kama su,” in ji shi.

Majalisar Dokokin Bauchi Ta Gargadi ’Yan Kwangila Bisa Aikata Ha’inci

Da ya koma kan batun Direbobin da ke hannun ‘yan bindiga  kuwa, shugaban, ya tabbatar da irin kokarinsu don ganin an ceto su da fasinjojin da suke tare.

Kuma shugaban ya karyata wasu kafofin yada labarai masu cewa, direbobi photo voltaic shiga yajin aikin zirga-zirga a fadin Jihar ta Zamfara.

Yana mai cewa, al’ummar yankin Masarautar Dan Sadau ne suka yanke shawara hana zirga-zirgar ababen hawa, saboda yadda maharan suka addabe su, wannan ne ya sanya mambobin mu suka mara masu baya domin muma ta shafemu, akwai direbobi uku na yankin a hannun maharan.

Akan haka ne shugaban ya yi kira ga al’ummar Jihar Zamfara da su ci gaba da yin addu’a don ganin Allah ya kawo mana karshen mawuyacin halin da muke ciki na wannan na matsalar tsaro.

What's On Your Mind?