Nura M Inuwa Ya Bawa Mutane Mamaki A Wannan Lokaci, Wani Abu Sai Baiwa

- Advertisement -


Labaran Kannywood Na Wannan Makon Mun Leka Zuwa Masana’antar Kannywood Inda Munkayi Kicibis Da Cewa, WAƘA baiwa ce da ba kowane mutum ke da ita ba. Duk wanda zai iya zama ya tsara ko ya rera waƙa, wannan mutumin na da matuƙar baiwa. Idan har akwai mutane na musamman keɓantattu, to mawaƙa ne.
Fasahar da ke cikin tsararriyar waƙa ta wuce duk yadda ake tunani. Wani zai ɗauka abin da ake buƙata a waƙa kawai ƙafiya ce. Da ita ne ma kawai su ke auna haɗaɗɗiyar waƙa. Ba haka ba ne, amma dai ƙafiyar na ɗaukar kaso mafi tsoka idan da za a karkasa da bai wa kowane tsari da salon waƙa maki.

Kusan duk mawaƙan Hausa sun ƙware ainun wajen tsara waƙa da sarƙa ta da haɗaɗɗun ƙafiya. Ya na daga kyakkyawan misali idan mu ka duba wata waƙar bege da Umar Abdul’azeez (Fadar Bege) ya yi, lokacin ya na da rai, inda ya ke wa Allah maɗaukakin Sarki kirari kamar haka:

“Ka kaɗaita abin bauta mai riƙe lamari na,Allah buwayi ina roƙo don isar Annabi na,Ka ƙara haske a harshe na da zan yaba wa gwani na,Kai ka ke yadda duk ka ga dama kar ka shafe batu na,Roƙo na ke yi da babbar murya ya maji roƙo na,Tsira aminci ka ƙara wa uban dukkan alami na,Mahmudu wanda ya sauka a Makka sannan ya koma Madina.”

Wani abin mamaki da Fadar Bege shi ne wasu baitukan a majalisi ya ke yin su da ka (wato a lokacin ya ke ƙirƙira.)

Nura M. Inuwa ya na rera sabuwar waƙar sa ta ‘Garƙami Wandon Ƙarfe’ ga dandazon masoyan sa a wasan da ya yi a filin Trade Fair na Kano ranar Talata da ta gabata

A ɗayan bangaren na mawaƙa, idan mu ka kalli Nura M. Inuwa, sai duk wani lissafi ya birkice. Nura ya yi ƙwarewar da ya ke iya juya waƙa yadda ya so. Ko da yake wasu za su iya cewa ai ya na samun isasshen lokaci ne na tunani da tsari, shi ya sa waƙoƙin ke kyau. Ko ma dai yaya ne, ya iya. Sannan a duk lokacin da ya saki album, ana ajiye waƙar kusan kowa ne, a saurari tasa. Saboda ya iya.

Dangane da ƙafiya a waƙa, bari ka ji yadda shi ya ke yin ta da salo, wanda ba kowa ke yi ba. Mu ɗauki misalin wannan waƙar da baitin ta ya fara:-

“Ke ce ta fari zo gimbiya amarya,Haƙuri za ki yi komai da lokaci ga shi naki ya zo mai fari na hali.”

A wannan waƙar ya saki fasahar da keta tunani, yadda ya ke jan dogon baiti masu sarƙaƙiyar da bagware ba zai iya biyawa ba. Misali:

“Gatan tuwo miya ce ba da wai ba a daka a raya jure hakan waye ne saman ki kalwa?Kanwa uwar gami, ke ce ƙure wa masu zunɗen ki sun manta sun yi shuka idon makwarwa.Na yo batun a da can mun ji kwalla ta fi fanteka, zurfin tukunya ma ba ya kai na garwa.Aiki da hankali ba kamar ƙwaƙwalwa ku yi ta yin shewa kar ku yi rayuwa wacce za ta zamto kamar kashin dankali.”

A misalin wannan baitin, kalmar “wa” ce ƙafiyar da ya yi amfani da ita. Ba kuma yadda ta ke hawa ba ne abin burgewa. Yadda a ƙarshen baitukan ya ke kuma shigar da ƙafiyar a duk inda aka samu saukar sauti ko hawa. Kamar dai wajen da ya ce “ƙwaƙwalwa” da kuma “shewa”.

Daga ƙarshe kuma ya na ƙare kowane baiti da kalmar ‘li’ saboda ita ce ƙarshen amshin farko, ‘hali’.

*Bamai Dabuwa Kirikasamma, wanda marubucin zube ne kuma mai sharhi kan rubutun zube, mazaunin Jihar Jigawa ne.

Domin Samun Sabbin Labaran Kannywood Akan Lokaci Ku Kasance Tare Damu A Wannan Shafin.

- Advertisement -