NSCDC Za Ta Hada Hannun Da Sojoji Don Samar Da Tsaro A Jihar Legas

0
106

NSCDC Za Ta Hada Hannun Da Sojoji Don Samar Da Tsaro A Jihar Legas

Shugaban runduna ta 81 ta sojojin Nijeriya da ke Legas, Maj.- Gen. Lawrence Fejokwu, ya kara bayyana aniyar rundunar sojojin Nijeriya na yin aki tare da hukumar NSCDC don samar da cikakken tsaro a jihar Legas gaba daya.

Shugaban rundunar ya bayyana haka ne a yayin ziyararsa ga shugaban hukumar NSCDC na yankin Legas ranar Alhamis.

Ya ce, sojojin a shirye suke su yi aiki tare da NSCDC don fattakar da bata gari masu yi wa tattaln arizkin kasa zagon kasa a jihar.

Ya kuma ce, wannan aikin hadin kan yana da matukar mahimmanci musamman a wannan lokacin da kasar nan ke fuskantar matsalolin tsaro da dama a sassan tarayyar kasar nan.

Ya kuma yaba wa NSCDC, reshen jihar Legas akan yadda suke gudanar da sintiri na tsawon awa 24 a wuraren da ke fama da matsaar tsaro.

“Da farko ina mai yaba wa shugaban rundunar NSCDC na yankin Legas karkashin jagotcin Mr Paul Ayeni, akan kokarin rundunar na kare dukiyoyin gwamnati a fadin jihar.

A nasa jawabin, shugaban NSCDC ya yaba wa shugaban rundunar akan ziyarar da ya kawo masa ya kuma yi alkawarin aiki tare da sojojin wajen fattatakar ‘yan ta’adda a a jihar Legas.

Ya kuma yaba wa sojojin akan yadda suke daukar dawainiyar horar da jami’an rundunur a duk lokacin da aka bukaci haka.

 

What's On Your Mind?