NSCDC Ta Kafa Kwamitin Binciko Zargin Karbar Naira Miliyan Daya Kudin Beli A Kebbi

0
146

NSCDC Ta Kafa Kwamitin Binciko Zargin Karbar Naira Miliyan Daya Kudin Beli A Kebbi

Daga:Umar Faruk Birnin-Kebbi

Hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) ta ce ta kafa wani kwamiti na mutum biyar da zai binciki zargin cin hanci da rashawa na karbar Naira Miliyan daya da ma’aikatanta suka yi a Jihar Kebbi.

Kwamandan NSCDC a jihar, Alhaji Suleman Ibrahim, ne ya bayyana haka lokacin da ya ke zantawa da wakilin MOBILIZED9JA A Yau kan abin da ake zargin wasu jami’an hukumarsa da aikatawa a Birnin Kebbi.

Ya ce, “Na karanta wani rahoton a yanar gizo cewa ana zargin jami’ammu da karbar cin hancin kudi har Naira Miliyan daya ga wani da ake tuhuma da laifin shigowa da man gasoline a cikin Jihar.

“Wannan bai taba zama al’adar jami’an tsaron NSCDC da masu ba da kariya ga farar hula a jihar ba. daya daga cikin abubuwan da muke da su shi ne yin aiki da gaskiya, gaskiya da taka tsan-tsan, yayin hulda da masu laifi.

“Ban shiga cikin wannan lamarin ba kuma ban san da hakan ba, sannan ina shakkar a ce wani jami’ina zai aikata wannan aikin ba bisa ka’ida ba, amma yanzu zan tabbatar da na dauki duk wani mataki don tabbatar zargin da ake yi wa jami’an jihar ta Kebbi a karkashin jagorancina. Saboda haka kwamitin mutum biyar zai gudanar da bincike na ba sani ba sabo duk wanda kwamitin ya kama da laifi tabbas dokar aikin NSCDC za ta yi aiki kansa,” in ji Kwamandan.

Ibrahim ya sha alwashin cewa duk wanda aka samu ya karbi kudi ga laifi tabbas za a hukunta shi yadda doka ta tanada.

Tun da farko lokacin da yake zantawa da manema labarai, mai rarraba Man Fuel (AGO), Mista Jimoh Abdulmumin, wanda ma’aikaci ne na kamfanin Chidi International Oil and Fuel, Abuja, ya nemi a kawo musu dauki.
Shiga tsakani na Kwamandan-Janar na NSCDC kan zargin karbar kudi Naira miliyan daya daga jami’an hukumar na jihar kebbi.
Abdulmumin, ya yi zargin cewa wasu jami’an rundunar solar cafke shi tare da direban babbar motarsa a lokacin da suke rarraba kayayyakinsu ga kwastomominsu a garin Jega mako guda da ya gabata.
“Makon da ya gabata, wasu jami’an tsaro na farin kaya na NSCDC a jihar kebbi a karkashin jagorancin wani Yarima Maigari solar kama ni tare da babbar motata dauke da Man AGO Fuel, wacce ba haramtacciya ba ne, kuma muna tare da takardun da suka dace ga doka.

“Amma solar yi ikirarin cewa samfurin ya kasance jabu kuma takardu na jabu ne.
“Solar tsare ni a Sel din shelkwatarsu, da ke GRA Birnin Kebbi har tsawon kwanaki uku. Lokacin da suka ci gaba da yi mana barazanar ci gaba da tsarewa, sai muka fara tattaunawa daga Naira 200,000 amma Yarima ya ce ba zai karbi kasa da miliyan daya ba in har muna so a sake mu saboda kwamandan jihar shi ma za su bashi na shi rabon daga cikin kudin.

“Bayan matsin lamba daga gare shi, maigidana ya nemi in kira daya daga cikin kwastomanmu
a Jega don ya zo ya roke shi kuma Yarima ya ki barin mu.

“Ya sha alwashin cewa za a ba kwamandan nasa kudin; kuma tun da kayanmu da motocinmu suna nan daram a filin Idi a Birnin Kebbi, sai muka yanke shawarar basu abin da suke so kada kasuwancin mu ya wahala.

“Na tambayi wani hadimin a otel din da na sauka a karamar hukumar Jega ya kawo mani tsabar kudi Naira Miliyan domin Yarima ya ki yadda da a tura masa ta asusun ajiyar bankinsa.

“Yaron ya kawo masa kudin, ya sake cafke yaron, sai da muka biya N10,000 kafin ya bar yaron ya tafi.

“Wannan shi ne dalilin da ya sa, muke neman shiga
Kwamanda-Janar na Cibil Defence ya shiga tsakani na da jami’ansa na jihar ta Kebbi da kuma masu ruwa da tsaki kan lamarin,” in ji Mista Jimoh Abdulmumin.

What's On Your Mind?