NIS Ta Fara Aiki Da Sabon Kundin Biza Na 2020

0
61

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) Muhammad Babandede MFR ya bayyana wa al’ummar kasa da kuma sauran baki ‘yan kasashen waje cewa an fara amfani da sabon kundin biza bisa amincewar Ministan Cikin Gida, Ogabeni Raug Aregbesola.

NIS Ta Fara Aiki Da Sabon Kundin Biza Na 2020

Sabon kundin bizar an tsara shi ne ta yadda zai saka karamcin da ke tsakanin Nijeriya da kasashen duniya.

A wata sanarwar manema labarai da Jami’in yada labarun NIS, DCI Sunday James ya fitar, CGI Babandede ya yi kira ga masu ruwa da tsaki kan sha’anin da sauran hukumomin da abin ya shafa su ziyarci adireshin e mail na hukumar www.immigration.gov.ng domin samun cikakken bayani da sabon kudin bizar da aka sa na kowace kasa da kuma ire-iren bizar da za a nema.

Kiris Da Gwamnatocin Baya Sun Rusa Nijeriya

Sabon kundin bizar wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a ranar 4 ga Fabarairun 2020, ya fara aiki ne daga 1 ga Oktoban 2020.

What's On Your Mind?