NIS Ta Dakatar Da Yin Sabon Fasfo Har Sai…

- Advertisement -

NIS Ta Dakatar Da Yin Sabon Fasfo Har Sai…

Daga Abdulrazak Yahuza Jere

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa ta dakatar da karbar bukatun masu neman yin sabon fasfo ko sabuntawa daga ranar Talata 18 ga Mayun 2021 har sai zuwa 31 ga watan domin ta samu damar biyan bashin da ya taru mata na fasfon.

Shugaban hukumar CGI Muhammad Babandede ya bayyana haka a ranar Talata a wani taron manema labaru da ya gabatar a shalkwatar hukumar da ke
Sauka, a kan hanyar filin jiragen sama na Abuja.

Babandede ya ce solar yanke shawarar daukar wannan matakin ne bisa umarnin Ministan Cikin Gida Rauf Aregbesola.

Wanda ya bukaci a kammala sallamar wadanda suka riga suka gabatar da bukatar fasfon a baya kafin a ci gaba da yin sabbi da sabuntawa wadanda nasu ya kammala aiki.

Za mu kawo muku cikakken labarin a jaridarmu ta MOBILIZED9JA A Yau ta gobe Laraba

- Advertisement -