Nijeriya Za Ta Shiga Matsala Idan Muka Zabi Shugaban Da Bai Dace Ba A 2023 – Dogara

0
92

Nijeriya Za Ta Shiga Matsala Idan Muka Zabi Shugaban Da Bai Dace Ba A 2023 – Dogara

Daga Yusuf Shu’aibu

Tsohon shugaban majalisar wakilai na tarayya, Mr Yakubu Dogara, ya bayyana cewa da wannan matsalolin rashin tsaro da Nijeriya take fuskanta a halin yanzu, wasu bangarorin kasar nan solar fada cikin rashin dai-daituwa. Tsohon shugaban majalisar tarayya ya kara da cewa, Nijeriya tana yaki da kanta, kafin lamarin ya ta’azzara ya kamata a yi wa tokan hanci, dole ne ‘yan Nijeriya su canza hanyoyin tunani da kuma yadda suke gudanar da abubuwanasu.
Da yake jawabi wajen yaye dalibai karo na 10 a jami’an Achiebers da ke Owo cikin Jihar Ondo a ranar Asabar, Dogara ya bayyana cewa, matsalolin da ke damun kasar nan a halin yanzu ba a taba zaton hakan ba, yana gargadi a kauce wa wadannan matsaloli domin kar su kazanta a cikin kasar nan ta yadda za su yi wahalar shawo kan bakin zaran.
Ya ce, “yankin Kudu-Maso-Yamma da yankin Kudu-Maso-Yamma su ne sabbin yakunan da ke fama da rashin dai-daituwa a Nijeriya. Idan aka hada wannan da mummunan rikice-rikice kamar irin na mayakan Boko Haram a yankin Arewa-Maso-Gabas wanda ya yi sanadiyyar daukan rayukan miliyoyin mutane masu yawa da na ‘yan bindiga a yankin Arewa-Maso-Yamma da fashin bakin teku da sauran laifuka a yankin Kudu-Maso-Kudu da rikicin manoma da makiyaya a wasu bangarorin kasat nan.
“Tare da rashin aikin yi wanda ya kai na sama da kashi 30 da durkushewar tattali arzikin da tsanani da karuwar rashin tsaro da karuwar raguwar cibiyoyin tsaro da tsanani talauci da rarrabuwar kai a tsakanin gwamnatoci, ya kamata a samo hanyoyin magance wadannan matsaloli.”
Dogara ya ci gaba da cewa, masana suna danganta rashin tsaro a Nijeriya da gazawar gwamnatin ko rashin gudanar da ayyukan gwamnatin yadda ya dace na samar da ababen extra rayuwa wadanda mutane suke bukata. Ya ce, lallai wadannan abubuawa cikin sauki suke fusata mutane har su fada cikin abubuwan da ba su dace ba.
“Haka kuma, rashin dai-daituwa da rashin adalci wajen bayar da mukamin da nuna bangaranci a tsakanin mutane musamman ma matsa masu saurin daukan fushi da zafin kai.
“Rashin hadin kan matasa a cikin kasar nan yana shafar ci gaban matasa wanda shi ne makasudin rarrabuwar kai.
“Kar mu sake mu tafka kuskure a zaben shekarar 2023, idan muka yarda muka tafka kuskure, to zai shifi cin nasararmu wanda za mu kwashe shekaru hudu muna cikin kunci, wanda zai iya janyo yaki da tashin hankali da kashe-kashe. Muna rikon Allah ya tsare mu,” in ji tsohon shugaban majalisar wakilci ta tarayya.

What's On Your Mind?