Nijeriya Za Ta Buga Wasa Da Kasashen Kamaru Da Mexico

- Advertisement -

Nijeriya Za Ta Buga Wasa Da Kasashen Kamaru Da Mexico

Daga Abba Ibrahim Wada

Tawagar Tremendous Eagles ta Nijeriya za ta buga wasan sada zumunta da kasashen Kamaru da Mexico a Turai da Kudancin Amurka, duk da fama da rashin kudi da hukumar kwallon kafar kasar nan ke fama.

Kocin tawagar kwallon kafar ta Najeriya, Gernot Rohr na bin hukumar bashin albashin wata shida da ba a biya shi ba kuma duk da fama da rashin kudi da take fuskanta, NFF ta tsara wasan sada zumunta da Tremendous Eagles za ta kara da tawagar Kamaru a birnin bienna na kasar Austria ranar four ga watan Yuni.

Haka kuma Najeriya za ta kece raini a wasan sada zumunta na biyu da Mexico a birnin Los Angeles na kasar Amurka wata daya tsakani a karawa da Kamaru kuma a watan Janairu shugaban hukumar kwallon kafar Najeriya, Amaju Pinnick ya ce yana ta fafutukar ganin ya biya dukkan bashin da ake bin hukumar.
‘Yan wasan Tremendous Eagles na bin bashin ladan wasanni da alawus alawus da dama, ya yin da mai horar da masu tsaron raga, Alloy Agu ke bin bashin albashin watanni 17 wanda har yanzu ba’a biya shi ba.

Nijeriya ta shirya wasannin sada zumuntar ne domin tunkarar karawar neman shiga gasar cin kofin duniya ta shekara ta 2022 da za ta yi a cikin watan Satumba wanda hakan yasa take ganin akwai bukatar shirya wadannan wasanni.
A shekarar bara Rohr ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da jan ragamar Tremendous Eagles da sharadin lashe kofin nahiyar Afirka na gaba da samun gurbin gasar kofin duniya da za a yi a katar.

Wannan shi ne wasa na shida da Najeriya za ta fafata da Mexico a manyan karawa, inda hudu daga ciki suka tashi canjaras sannan Mexico ta yi nasara a kan Tremendous Eagles da ci 2-1 ranar 24 ga watan Yunin shekara ta 1995 a US Gold Cup a birnin Tedas na Amurka.

- Advertisement -