Ni ba dan ta’adda bane, Direbana da Sakatarena duk Kiristoci ne, kuma nafi daukar Kiristoci aiki fiye da Musulmai – Sheikh Pantami

0
219

Ni ba dan ta’adda bane, Direbana da Sakatarena duk Kiristoci ne, kuma nafi daukar Kiristoci aiki fiye da Musulmai - Sheikh Pantami

Ministan Sadarwa da tatalin arzikin Zamani, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa, maganar da ya taba yi aka kungiyoyin Taliban da Alqaeda ba’a fahimceshi bane.

Ya kuma kara da cewa, ba’a fahimceshi bane dan kuwa Direbansa da me taimaka masa na musamman da Sakatarensa duk kiristocine.

Ummi zee zee Tayi Martani Mai Zafi Zuwa Ga Yan Arewa Musulmai Akan Damfararta Da Ankayi Naira Milliyann 450

Ya bayyana hakane a ganawarsa da da Individuals’s gazette inda ya bayyana cewa sunan Direbansa Mai Keffi wanda kuma Kirista ne me rike addininsa da kyau. Yace hakanan kuma Sakatarensa, Ms Nwosu Kiristane, sai kuma Dr. Femi wanda shima Kiristane dake aiki dashi a matsayin me taimaka masa na musamman.

Yace da baya son Kiristoci da ba zai daukesu aiki ba, yace yana daukar Kiristoci aiko fiye da Musulmai saboda yana amfani da kwarewa maimakon kabilanci da nuna banbancin bangaranci.

Yace bai taba goyon bayan ta’addanci ba kuma yakan yi wa’a zi akan a gujeshi sannan kuma yan kiran a yi zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-daban.

What's On Your Mind?