Ngige ya ce za a iya la’akari da UTAS a madadin IPPIS wajen biyan Jami’o’i

0
69
  • Gwamnati ta yi maganar yiwuwar karbar manhajar UTAS a madadin IPPIS

  • An kama hanyar samun maslaha a yajin aikin da Malaman jami’an su ke yi

  • Za a gabatar da UTAS a gaban AGF, NITDA, da NSA kafin a amince da manhajar

A ranar Talata, 13 ga watan Oktoba, 2020, gwamnatin tarayya ta ce ta na duba yiwuwar karbar manhajar UTAS da kungiyar ASUU ta gabatar.

Kungiyar malaman jami’a ta ASUU ta gabatar da UTAS a gaban gwamnatin tarayya, a matsayin madadin manhajar nan ta IPPIS ta biyan albashin.

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi la’akari da abin da ASUU ta zo da shi. Wannan sanarwa ya fito ne daga bakin Ministan kwadago, Dr. Chris Ngige.

Ngige ya ce za a iya la’akari da UTAS a madadin IPPIS wajen biyan Jami’o’i

Jaridar Premium Instances ta bayyana cewa Chris Ngige ya bayyanawa ‘yan jarida wannan ne bayan zaman sa’a biyu da ASUU ta yi da majalisar dattawa.

 

Ngige ya ce a nan gida aka kirkiro manhajar da aka zo da shi, don haka ta cancanci a jarraba ta.

“Mun yarda bayan taron cewa mu yi la’akari da UTAS da aka zo da shi a madadin dabbakar da manhajar IPPIS da ke ta kawo mana matsaloli.” Inji sa.

Ngige ya ce: “Ba mu yi watsi da IPPIS gaba daya ba, kuma ba mu karbi UTAS kaco-kam ba.”

Dr. Gawuna Ya Jinjina Wa Kungiyar Lauyoyin Da Ke Taimaka Wa Mai Karamin Karfi

Ministan ya ce daga nan za a kai wa NITDA manhajar domin ta duba, sai kuma a tafi NSA.

A farkon makon nan kun ji cewa Kungiyar ASUU ta yi wata ganawar sirri da shugabannin majalisar dattawa a game da sabaninsu da gwamnati.

Bayan zaman da aka yi, Ahmad Baba Kaita ya tabbatar da cewa ana neman kai ga maslaha.

What's On Your Mind?