Yahaya Nasko – Neja Za Ta Samar Da Audugar Da Ba A Yi Tsammani Ba

0
56

MALAM YAHAYA BALA NASKO shi ne jami’i mai sanya idanu akan noman auduga a Jihar Neja. A hirarsa da Wakilin MOBILIZED9JA A YAU, MUHAMMAD AWWAL UMAR, ya bayyana irin wahalhalun da su ka sha a wannan shekarar kan noman auduga da hanyar da su ka bi wajen shawo matsalar.

Neja Za Ta Samar Da Audugar Da Ba A Yi Tsammani Ba

Ga hirar a takaice:

Kai ne jami’in da ke sanya idanu ga manoman auduga na kungiyar manoman auduga NACOTAN a takaice, shi ya ka ke kallon yadda manoman suka karbi shirin na babban bankin Najeriya?

Da farko mu na nuna godiyar mu ga Allah da ya sanyawa gwamnatin kasar nan tunanin dawo da martabar noman auduga wanda yanzu haka a shekarar bara da aka fara gabatar da harsashen shirin, manoman a jihar Neja yankin kasar Bargu mutane kusan dari biyu ne suka anfana da tallafin, bayan ganin yadda suka nuna kwazo jihar nan itace ta hudu a kasar nan a bara, wanda shi ya janyo babban bakin Najeriya da aka damka kula da harkokin shirin samun kwarin guiwar kara adadin manoman auduga daga dari da arba’in da doriya zuwa sama da dubu hudu a wannan shekarar ka ga wannan bakaramin nasara ba ne babba.

Maganar matsala dai ba mu fuskance shi mai tsanani ba, illa a yankin kasar Bida mun dan samu matsalar shuki kuma saboda karancin ruwa a wancan lokacin yasa shukin bai fito ba, domin bayan shukar an samu kusan wata daya ba a yi ruwan sama da ya janyo mutuwar wasu iraruwan a cikin saboda da rashin samun ruwa a ‘yan watannin baya, da yanzu haka mun shawo kan lamarin, sai kuma wadanda aka baiwa irin da bai dace ba, kuma laifin daga masu kawo irin ne.

A gaskiya NACOTAN ta na farin ciki gaya kan yadda manoma suka karbi shirin da yadda suka himmatu dan cika wannan alkawalin, domin kamar yadda na fada ma tun farko ni ne jami’in da ke sanya ido kan yadda manoman ke tafiyar da noman a halin yanzu, kuma kusan dukkanin kananan hukumomin da na ziyarci gonakin su na yi farin ciki da yadda na ga lamarin na gudana.

Kalli Bidiyon Aisha Tsamiya Tana Nuna Alamomin Yin Aure

A baya ana samun rahotannin yadda ake baiwa manoma tallafin a karshe suna sayarwa, shin ko a wannan karon hakan ya faru?

Gaskiya ne, amma tun bayan karban shugabancin Alhaji Abubakar Shiyaki da sakatarensa, Amb. Dakta Nura Hashim ba mu samu wannan rahoton ba, domin ba wani manomin da mu ka yarda aka ba shi wannan tallafin kai tsaye sai ta hanyar kungiya, sannan kafin mu amince a ba su kamar yadda CBN ta umurce mu sai da mu ka zauna da su aka wayar masu da kai, aka nuna masu alfanun shirin, wanda duk aka tantance ya san da hakan kuma ya amince da hakan.

Saboda haka maganar sayar da kayan bayan manoman photo voltaic karba ba mu fuskance shi ba. Kowani manomin da ya ci gajiyar shirin muna da jami’ai a dukkan sassan jihar da ke sanya ido, muna bin su sau da kafa muna ba su shawarwari wanda a halin da ake ciki yanzu bayan an shuka audugar ta fara tsira wasu wuraren ma audugar ta fara fitar da hure da ta ke nuna alamar tana bukatar feshin magani wanda shi ma mun baiwa manoman irin maganin da ya dace ayi feshin da shi.

A baya mun san irin audugar da ake shukawa tana bukatar ruwan sama sosai, shin ko irin wannan audugar ne ku ka bayar a wannan karon? Kasan auduga kala biyu ce, muna da wadda mu ka sani a baya baka ce kuma tana da girma, amma wannan sabon iri ne aka yi oda wadda ta dace da yanayi mai sauki, za ka ga kwarorinta kananan kuma yana da haske, bai da wahalar noma kamar wadda mu ka saba da ita a baya, yanzu bayan wannan ta damuna akwai ta rani ma da za mu bayar nan ba da jimawa ba.

A matsayin kungiyar ku ya ku ke kallon wannan shirin dawo da martabar noman auduga a jihar nan?
Gaskiya shiri ne mai kyau, domin zai taimaka a bangarori da dama, musamman hanya ce ta dawo da martabar kasar nan wajen samun nasarar karfafa guiwa ga jama’a na samun aikin yi, dawo da martabar kasuwancin auduga ne kamar yadda aka san mu a baya a idon duniya. Sannan ita kan ta gwamnati zai taimaka mata wajen yunkurin ta na farfado da masana’antu da kuma dawo da martabar kasuwancin suturun mu mai makon yadda ake shigo da su daga wasu kasashen duniya, kai a takaice za mu yi kafada da kafada a kasuwancin duniya ta hanyar sutura.

Shin ko ka na da wata shawara ga manoman auduga?
kwarai kuwa, ya kamata duk wanda ke sha’awar sana’ar nan ta noman auduga ya tabbatar ya tuntubar kwararru a fannin aikin gona. Sannan idan Allah yasa an noma a rika tuntubar kungiya kan yadda za a yi kasuwancin saye da sayarwa. Hakan zai taimaka wajen fadawa hannun wadanda ba su da ce ba masu kokarin karye guiwar manoma, domin ireirensu ba abinda suke yi illar cutar da manoma, amma hanyar da gwamnati ta dauka yanzu ta hannun babban bankin kasar nan shi ne samar da kamfanonin da zasu rika sayen audugar daga hannun manoman kai tsaye.

A kungiyance bisa al’ada akwai kungiyoyin da ke anfani da damar su wajen aljihun mambobin su, shin haka abin ya ke gare ku?

Allah cikin ikonsa bisa jagorancin Alhaji Abubakar Shiyaki da sakatarensa Amb. Dakta Nura Hashim photo voltaic zage ba dare ba rana wajen kare hakkin mambobin mu, ina fada maka da irin wannan shugabancin mu ke da shi tun farko da manoman auduga ba su yi kasa a guiwa ba, domin duk wani abinda za a yi a kungiyan ce babu wani abinda suke boyewa, kuma a kowani lokaci idan suka hango wani karuwa da manban NACOTAN zai samu a tsaye suke akan shi, wanda muna anfana da kokarin su gaya.

Yanzu wani shawara za ka baiwa kungiyar ku, manoma da ita gwamnatin?

Da farko zan fara da manoma, ya kamata kamar yadda suka kuduri aniyar noman auduga to kar su karaya, su tsaya tsayin daka wajen samun nasarar abinda suka sanya a gaba. Na biyu kuma su rika tuntubar kwararru a fannin noman auduga ta haka ne duk wani abinda ya daure masu kai za su fahimce kuma su ka’idodin da ake ba su wajen ganin ba su yi aikin banza ba.

Dangane da ita kungiyar kamar yadda shugabancin kungiyar ya kyautata niyya wajen sanya danba da fitar da jihar nan kunya a idon duniya, to kar su ja baya sannan su cigaba da taimakawa manoma da duk shawarwarin da suka da ce, domin ina da tabbacin nan gaba kadan Neja za ta zama sahun gaba a noman auduga ganin yadda Allah ya hore mana kasar noma mai albarka, domin a cikin jahohin kasar nan muna sahun gaba, dan muke da yanayin noman damuna mai albarka, sannan muna da yanayin noman rani ba tare da an sha wahala an kashe kudi sosai ba a dukkanin tsoron da ka san ana sanya shi a kasa.

What's On Your Mind?