Neja Ce Kan Gaba Wajen Fuskantar Matsalar Masu Garkuwa Da Jama’a- Gwamna Bello  

0
74

Neja Ce Kan Gaba Wajen Fuskantar Matsalar Masu Garkuwa Da Jama’a- Gwamna Bello  

Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya bayyana cewar  jiharsa ce kan gaba a jahohi bakwai da ke fuskantar matsalar masu garkuwa da jama’a da wasu miyagun ayyuka a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mika takardar kama aiki ga sabon sarkin Kagara, Alhaji Ahmed Garba Attahiru na biyu a matsayin sarkin Kagara mai daraja.
Gwamna Sani Bello ya bayyana cewar nadin Ahmed Garba shiri ne daga Allah wanda ba wani da zai hana faruwar hakan a lokacin zaben sabon sarkin, ya bayyana cewar ya umurci masu zaben sarkin a masarautar Kagara da su yi zabe ba tare da an yi masu katsalandan ba wanda ya haifar da samun nasarar Ahmed Garba Attahiru Gunna a matsayin zababben sarki.

Gwamnan ya nusar da sabon sarkin da ya kiyaye nauyin da ya rataya a wuyansa, yayi shugabacin da gaskiya, wajen tafiya da kowa, ta hanyar fahimtar cewar shi yanzu uba ne na al’umma.

” Ina tsammanin sabon sarkin ya fahimci cewar ba ni na zabe shi ba, Allah ne ya tabbatar da shi akan wannan karagar, wannan ne dalilin ne zai sa ya zama uba ga kowa a masarautar Kagara,” a cewarshi.

NOA Da UNICEF Sun Hada Kai Don Kawo Karshen Cin Zarafin Mata Da Kananan Yara A Jihar Jigawa

Gwamnan ya janyo hankalin sabon sarki akan matsalar tsaro musamman a yankinsa, kuma ya neme shi da ya hada kai da al’ummarsa na masarautar koda za a rika daukar matakai a fada dan shawo kan matsalar.

Gwamnan ya shawarci mahara masu garkuwa da jama’a da masu taimaka masu wajen kai hare hare ga jama’a da su ajiye wannan dabi’an su canja su koma mutanen kirki.
Gwamnan yayi addu’ar Allah da ya baiwa sabon sarki wannan matsayin da ya taimaka masa, ya kare shi ya kuma ba shi ikon sauke wannan nauyin.

What's On Your Mind?