NEDC Za Ta Aiwatar Da Ayyuka 35 A Jihar Taraba

- Advertisement -

NEDC Za Ta Aiwatar Da Ayyuka 35 A Jihar Taraba

Hukumar bunkasa shiyyar Arewa Maso Gabas (NEDC) kwanan nan za ta fara aiwatar da wasu ayyuka guda 35 a Jihar Taraba, kamar yadda kwamishina a hukumar Chief Dabid Kente ya shaida.

 

Kente wanda ya shaida hakan a ranar Lahadi lokacin da ke magana da ‘yan jarida a Jalingo, ya kara da cewa ayyuka guda biyu-biyu za a gudanar a cikin kananan hukumomi 16 da suke fadin jihar.

Kwamishinan ya bayyana cewar nan da makonni uku masu zuwa ne za a fara aiwatar da wadannan ayyuka da yawansu ya kai guda 35 a dukanin kananan hukumomin jihar.

Yana mai bayanin cewa daga cikin ayyukan, za a gina manyan makarantun sakandari guda uku a yankunan mazabun sanatoci uku da suke jihar, yana mai cewa nan kusa kuma za a tura ‘yan kwangilar zuwa wuraren da za a gudanar da wannan aikin, kuma yana mai bayanin cewa dukkanin ababen da suka dace an tanadar domin ganin ayyukan solar samu tafiya yadda aka tsara kuma daidai da manufar hukumar.

“Mun kuma samar da tallafin karatu da sauran muhimman sashi da suke taimaka wa rayuwar al’umma,” ya kara bayaninsa.

Kente, ya hori jama’an da za a gudanar da ayyukan a yankunan da su tabbatar da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga ‘yan kwangilar da za a tura yakunansu domin samun nasarar gudanar da ayyukan nan cikin sauki.

Wakilinmu ya nakalto cewa ita dai hukumar NEDC gwamnatin tarayya ce ta kafa da zimmar samar da ayyukan da za su farfado da shiyyar arewa maso gabas bayan da hare-haren ‘yan Boko Haram ya daidaiya yankina.

- Advertisement -