NDLEA Ta Kama Muggan Kwayoyi Mai Nauyin Kilogram 2412.39 A Jihar Oyo

NDLEA Ta Kama Muggan Kwayoyi Mai Nauyin Kilogram 2412.39 A Jihar Oyo

Hukumar NDLEA ta samu nasarar cafke kwaya mai nauyin kilogram 2412.39 a samamen da ta kai sassan jihar Oyo a zango na uku na shekarar 2020.

Shugabar hukumar, Josephine Obi, ta bgayyaa haka a cikin rahoton da jami’ar watsa labaran hukumar, Mutiat Okuwobi ta raba wa manema labarai a garin Ibadan ranar Asabar.

Ta kuma kara da cewa, kwayoyin da aka kama photo voltaic hada da tabar wiwi, da Tramadol, Diazepam, Rohypnol, Colorado, codeine da sauran muggan kwayoyi masu cutar da al’umma.

Ta kuma kara da cewa, a cikin zangon da ake magana, hukumar ta kama mutum 37 wadanda suka aikata lafukka daban daban da suka shafi mu’amala da kwayoyi.

NOA Da UNICEF Sun Hada Kai Don Kawo Karshen Cin Zarafin Mata Da Kananan Yara A Jihar Jigawa

“An samu nasara daure mutum 31, hukuncin da ya tashi daga wata shida zuwa shekara 10 a gidan yari.

“Hukumar ta kuma samu nasara tsugunar da mutum 49 wadanda suka kamu da shan kwaya a jihar.

Ta kuma ce, rundunar ta lalata wasu manyan gonakin taba wiwi a kauyen Ajani da ke karamar hukumar Ona-Ara.

Ta kuma shawarci al’umma su kasnce a ankare tare da kuma bayar da bayanai masu mahimmanci da za su kai ga kama masu safarra kwayoyi a jihar.

 136 total views,  1 views today

About M. Jamiu 1079 Articles
Muhammed Jamiu is a Head Editor at Mobilized9ja (M9JA). He has been publishing for 8 years and focused more on Local/World News, Nigeria Music & Video all in English and Hausa Language.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*