NDE Na Koyar Da Matasa 100 Kan Kiwo Da Amfanin Gona A Bauchi

0
67

NDE Na Koyar Da Matasa 100 Kan Kiwo Da Amfanin Gona A Bauchi

Daga Khalid Idris Doya,

Hukumar samar da ayyukan yi ta kasa (NDE) a Jihar Bauchi, ta fara aikin horas da matasa 100 wadanda ba su da ayyukan yi koyon ilimin kiwon dabbobi da na amfanin gona na tsawon watanni uku.

Mataimakin Darakta a sashin bunkasa ayyukan yi a yankunan karkara na hukumar a Bauchi, Malam Inuwa Adamu shi ne ya shaida hakan a ganawarsa da ‘yan jarida jiya a Bauchi.

Adamu, wanda ke cewa horon an kirkireshi ne a karkashin shirin tabbatar da bunkasa noma da inganta koyar da shi (SADTS) na shalkwatar NDE, yana mai cewa shirin yana daga cikin tsare-tsaren da manufofin gwamnatin tarayya na kyautata harkokin noma da inganta abinci a fadin kasar nan.

Ya ce manufar shi ne koyar da matasa sabbin dabarun zamani na sarrafa amfanin noma, yana mai karawa da cewa horo ne na musamman da za a baiwa dukkanin masu cin gajiyar shirin ta yadda za su iya sarrafa kayan nomansu bisa fasahar zamani kuma cikin inganci.

Adamu, yana mai cewa horon na watanni uku, za a shafe makonni biyun farko ana koyar da daliban a karance a yayin da za a karasa sauran lokacin wajen koyar da su a aikace a kuma zahirance, “Matasa 100 wadanda suka kasance basu da ayukan yi ne ke cin gajiyar wannan shirin wadanda aka zakulo daga kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi.”

Ya kuma bayyana cewar muddin matasan suka maida hankali suka koyi wannan horon da ake basu yadda ya dace, za su samu tallafin rancen da zai agaza musu wajen kafa nasu harkokin kasuwancin ababen da suka koya.

Ya kuma ce NDE za ta samar musu da shaidar samun horon na musamman wanda zai iya basu damar samun rancen noma daga bankin gona ko shirin bankin NIRSAL Microfinance domin kyautata harkokin kasuwancinsu.

Shi ma da yake jawabinsa, shugaban sashin ayyuka na musamman na NDE A Bauchi, Sulaiman Abubakar, ya bayyana cewar hukumar a karkashin shirinta na (EBTS), ta zabo wasu matasa 40 da ake basu horo na musamman kan kula da muhallai na tsawon watanni uku.

Ya kuma ce za a baiwa masu samun horon naira dubu shida shida ga kowannensu a matsayin kudin sufuri da zai taimaka musu wajen halartar dukkanin oron a kowani rana.

What's On Your Mind?