Dogaro: NDE Na Bai Wa Mata Da Matasa 300 Horo A Bauchi

0
78

NDE Na Bai Wa Mata Da Matasa 300 Horo A Bauchi

Hukumar samar da aiyukan dogaro da kai ta kasa  (NDE) na kan baiwa mata Zawarawa da ‘yan Mata 300 horo na musamman kan sana’o’in dogaro da kai a sashin koyon hada sabulai, mayukan shafawa kala-kala, da dai sauransu da suka shafi Cosmetology a jihar Bauchi.

A lokacin da ke jawabi a yayin kaddamar da koyar da sana’o’in a Bauchi jiya, Darakta Janar na NDE Dakta Nasir Ladan Argungu ya ce muddin matan suka nutsu suka koyi horon yadda ya dace za su samu damar rike kawukansu da na iyalansu ta hanyar sarrafa abbaben da suka koya a fannoni daban-daban.

NDE Na Bai Wa Mata Da Matasa 300 Horo A Bauchi

Argungu wanda ya samu wakilcin Ko’odinatan hukumar a jihar Bauchi, Aliyu Lawan Yaya ya shaida cewar baya ga matan 200, akwai wasu karin matasa 100 da za su ji gaskiyar horo kan sana’o’in na musamman da suka kunshi dinki, wanda, sarrafa na’ura mai kwakwalwa, kafinta da kuma sauransu.

Argungu ya ce matan za su samu koyon sana’o’in ne na tsawon mako biyu kana za a ba su dan kudi domin ba su karfin halartar wajen koyon sana’o’in, yana mai nusar da su cewa su fa maida hankali su koyi ababen da ake son su koya domin muhimmancinsa a garesu, “A wasu wuraren sai mutum ya biya maguden kudade kafin a koya masa irin wadannan sana’o’in, amma ku NDE za ta baku ilimin kyauta don haka ku maida hankali domin a cimma nasarar da aka sanya a gaba,”

An sace amaryar mai gidan burodi a Katsina

Kan matasa 100 masu samun horo na musamman din, Darakta Janar din ya ce su za su dauki tsawon watanni uku ne suna samun horo kan sana’o’in da ake koyar da su, inda ya ce bayan kammala horon za su baiwa kowani matashi naira dubu biyar N5,000 domin karfata musu gwiwa.

Ya na mai cewa photo voltaic samar da kwararrun masu bada horon sai ya jawo hankalin masu cin gajiyar shirin da su yi kokarin amfana su da iyalansu.

Amina Haruna daya daga cikin masu cin gajiyar shirin ta sha alwashin maida hankali wajen koyon sana’o’in da ake koyar musu, tana mai nuna hakan a matsayin hanya da zai taimaka wa rayuwarsu, sai ta jinjina wa hukumar NDE bisa kokarinta na kyautata rayuwar mata da matasa ta fuskacin sana’o’in dogaro da kai.

What's On Your Mind?