Nazari A Kan Matsalolin Da Ke Tattare Da Tazarar Haihuwa

0
141

Nazari A Kan Matsalolin Da Ke Tattare Da Tazarar Haihuwa

Daga Sameerah Bello Shinko:

08025729364 [email protected],

Bahaushe yana cewa da haihuwar yuyuyu, gwanda d’a daya kwakwara. Wanda idan aka yi nazarin wannan maganar gaskiya ce, da ka haifi yara da yawa ka kasa tarbiyantar dasu har su zama mutanen kirki, gwanda ka haifi iya wadanda zaka iya bawa kulawa da sauke nauyinsu da ubangiji ya dora maka. Wannan na daya daga cikin dalilai da zamani ya zo mana da hanyoyi da dabaru na tsara iyali koma kayyade su.  Tsarin iyali da kaiyade su bahasi ne da aka dade ana  tayar da jijiyar wuya a kai. Hakan har ya haifar da sabani tsakanin addinai da mazhabobi, a daya bangaren kuma tsakanin al’ummu da gwamnatoci. Muhimmancin abun ne ya saka ni bayar lokaci nayi bincike a kan hakan da kuma yanda aka dauke sa a al’ummar mu ta Hausawa. In da zan yi bayani a kan ma’anarsa, dalilan yin sa, halaccin yin sa, da kuma hanyoyin yin sa.

Shin Menene Kayadde Iyali Da Tazarar Haihuwa?

Hukumar lafiya ta duniya WHO wato ‘world well being group’ ta bayyana tsarin iyali a matsayin wata hanya da ta baiwa iyali damar kayyade adadin yaran da suke so su haifa, ko kuma tazara tsakanin haihuwa; ta hanyar amfani da wasu hanyoyin hana daukar ciki. Shafin Wikipedia kuma ya fassara tsarin iyali ne a matsayin wani mataki na tsara yawan yaran da ya kamata a haifa ko kuma tazara tsakanin haihuwa ta hanyar amfani da wasu dabaru. Tsarin iyali dai ya kasu zuwa biyu, wato:

TAZARAR HAIHUWA: wannan na nufin bada tazara na a kalla shekara biyu daga haihuwa zuwa wata haihuwar. Kenan ya kasance sai an yaye yaro kuma ya yayi kwari yana cin abinci, kuma ya iya tafiya wata kila har da magana. Ta yanda ko kani za a masa ba zai sha wuya ba.
KAYYADE IYALI: wannan kuma yana nufin mutum ya zauna ya ce iya adadin yara kaza zai haifa a rayuwarsa,kuma daga kansu ba zai kara haifar wasu ba. Kaiyade Iyali zai iya zama wanda ya shafi mutum daya da gidansa, ko kuma tsakanin gwamnati da mutanen da take mulka: ta hanyar kafa wata doka da zata hana yaduwar dan adam da yawaitarsa da kaiyade yawan dan adam (misali kasar China information hana haihuwar fiye da yaro daya). Wannan shi ne abin da ake jayayya a kansa.

DALILAN YIN TSARIN IYALI

Binciken ya nuna cewar mata da yawa na muradin yin amfani da abubuwan tazarar haihuwa amma basa samun haka; ko dai saboda rashin bayanai da kuma ayyukan kiwon lafiya ingantattu, ko kuma rashin samun goyon baya daga mazajensu da ma al’ummar da suke zaune a cikin ta. Sai dai kuma bada tazarar yana da amfani sosai kamar haka:

Bada tazarar haihuwa yana taimakawa sosai don tabbatar da koshin lafiyar uwa da danta.
Yana taimaka wajen rage cututtuka da ke kama yara, kamar ciwon yunwa da a ke kira tamowa.
Yana kuma taimakwa wurin rage hadarin kamuwa da cututtuka da suka shafi bangaren tsabta, irin amai da gudawa.
Yana taimakawa mata wurin samun lafiya da kuzari kafin samun wata haihuwar.
Hakan na taimakawa iyaye wurin bawa yaransu tarbiya mai kyawu, su kuma kula da cin su, sha, sutura da ilimi babu takura.
Hakan na rage alkaluman mace-macen mata yayin haihuwa ko mutuwar yara kanana.
Yana taimakawa kaucewa yawan zubar da ciki da wasu ke yi saboda solar yi sa a lokacin da basu bukata.
Bada tazarar haihuwa muhimmin abu ne a bangaren lafiya ga mahukunta, hakan na taimaka musu wurin tsare-tsaren su na tsawon shekaru masu zuwa.

HALASCIN YIN TSARIN IYALI A A MUSULUNCI

Da yawa malam Bahaushe yana kafa hujja da cewar addini yace ayi aure a hayayyafa, Annabi Mohammadu (SAW) zai yi alfahari da hakan ranar al-Kiyama. Abinda suka kasa fahimta shi ne; ai Annabi  ba zai yi alfahari da yawan yu-yu-yu marasa amfani ba. Malamai da yawa solar fadi halacin bada tazara a haihuwa. Da yawan su suna kafa hujja da ayar nan da ke Magana a kan daukar ciki, shayarwa da kuma raino, in da ubagiji ke cewa  a cikin suratul( Al-bakara, aya ta 233).  “Kuma masu haifuwa (sakakku) suna shayar da abin haifuwarsu shekara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya cika shayarwa. Kuma ciyar da su da tufatar da su yana a kan wanda aka haifar masa da alheri. Ba a kallafa wa rai face iyawarsa. Ba a cutar da uwa recreation da danta, kuma ba a cutar da uba recreation da dansa, kuma a kan magaji akwai misalin wancan. To, idan suka yi nufin yaye, a kan yardatayya daga gare su, da shawartar juna, to babu laifi a kansu. Kuma idan kun yi nufin ku bayar da diyanku shayarwa, to, babu laifi a kanku idan kun mika abin da kuka zo da shi bisa al´ada. Kuma ku bi Allah da takawa. Kuma ku sani cewa lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatawa, Mai gani ne.”

Amma kuma solar ce haramun ne mutum ya kayyade adadin yaran da yake so ya haifa: mussaman idan hakan nada nasaba da tattalin arziki ko yawaitar al’umma. Saboda fadar ubangiji “kuma Allah ya halitta ku daga turbaya, sa’an nan daga digon maniyyi, sa’an nan ya saka ku surkin maza da mata. Kuma wata mace bata yin ciki, kuma bata haihuwa, face da sanin sa, kuma baza a rayar da wanda ake rayarwa ba, kuma baza a rage tsawon ransa ba face yana a cikin littafi. Lalle wancan mai sauki ne a wurin Allah.”(Al- fatir, aya ta 11).

HANYOYIN TSARA IYALI

Akwai hanyoyi ko dabaru da dama da ake bi wajen hana haihuwa ko kayyade iyali, wasu ma tun kafin bayyanar Shari’ar musulunci da matakin Tsara Iyali na zamani su bayyana. Wadannan ne hanyoyin da mutane suke dauka wajan kayyade ko tsara iyali wadanda solar hada da: –

Azalu: Shi ne mutum ya kauce daga matarsa yayin kwanciya ya fitar da ruwan maniyinsa wajan farjinta yayin kawowa.
Jinkirta aure: shi ne kin yin aure da wuri domin kada a haihu har sai mace ta kusa tsufa ta manyanta, tana mai shekaru masu yawa ta yadda da ta fara haihuwa shekarun da zata bar haihuwa zasu riske ta da wuri, Wannan ita ce hanyar da aka fi amfani da ita a Kasar Sin (Chaina)
Daina jima’i da mata baki daya domin sai an yi jima’i za a samu ciki da haihuwa.
Zubar da ciki: Wannan ita ce hanyar da ake dauka a mafi yawancin kasashe wato zubar da ciki ta hanyar shan magani ko wani abun na dabam.

Zamani kuma sai ya zo mana da hanyoyi kamar su:

Kwayoyin magani masu hana haihuwa (Oral Contraceptives (PILLS): wadannan kwayoyi ne da ake amfani da su don hana haihuwa, irin wadannan kwayoyi suna yin tasiri ne ga maniyyin mace su hana su aiki.
Allurar hana haihuwa (Injections): su kuma wannan allurai ne da akan yi don hana haihuwa. Daga cikin alluran da aka fi amfani da su don wannan aiki ita ce “Depo-provera medrody progestere Actate (DPMPA)”. Ita wannan allurar tana hana ciki ne ta wajen danne karfin kwayoyin maniyyin mace. Tana kuma kade jikin mahaifa ta yadda ko da ba ta yi tasiri ba kwan maniyyin ba zai sami in da zai makale a mahaifa ba, tana kuma tara majina mai kauri a hanyar da maniyyi kan wuce zuwa mahaifa, don kada ya samu wucewa. Akwai ta wata daya-daya, biyu-biyu zuwa uku-uku.
Zaren mahaifa (Intra Uterine Units (IUD): shi ma wata hanyar ce ta hana haihuwa. Wani zare ne na roba wanda akan sanya a mahaifa a bar shi sai zuwa wani dogon lokaci. Ba za a cire ba sai sanda matar ke son ta sake haihuwa. Wannan zare yana hana maniyyi kuzari ya kuma kashe kwayoyin maniyyi na mace da kwaroron da sukan bi zuwa mahaifa.
Robar mata (Diaphragms and Cervical Caps): Ita kuma wata roba ce mai tattausan baki. Ana saka wannan roba ne a cikin farji kafin saduwa ta yadda zai je ya toshe kofar mahaifa. Ana kuma shafa wani mai wa roban kafin a sa.
Robar maza da mata (condoms): wato kororon roba, shi kuma ana saka shine domin hana maniyi kai ga kwai, kamar da azilu ne na zamani.
Hanyar lissafin kwanakin haila: Ita ce lissafin kwanakin hailar mace da tabbatar da tsayaiyun kwanakinta na haila, domin gano kwanakin da kwanta yake sauka. Sai a nisanci wadannan kwanakin da kwana biyu kafin da bayan saukar kwan. Wato idan mace tana da haila tabbatacciya mai aiyanannun kwanaki tsayayyu to wannan matar ita wannan hanyar take yi wa amfani banda sauran mata. Sai a san kwanakin da take haila, to daga ranar da take fara haila zuwa ranar sha biyu ba ta daukar ciki amma daga sha biyu daga ranar da ta fara haila zuwa sha shida to a wannan kwanaki tana iya daukar ciki sai a nisanci kusantarta.
Juye mahaifar mata ko dandaka a maza: wannan kamar wata karamar fidace da a ke yi dan juye mahaifar mace a hanata daukar ciki har abada,ko a tsinke jijiyar da ke fitar da maniyi a jikin maza.

Wannan su ne hanyoyin da ake amfani da su wajan kayyade ko tsara iyali kuma ta yiwu akwai wasu hanyoyin da mu ba mu san su ba da wasu ke amfani da su. Yawancin wadannan hanyoyi da ake amfani da su musulunci ya halatta su sai dai wasu daga ciki da shari’a ta haramta kamar zubar da ciki. Malamai a Ilimin Usul na cewa komai halal ne sai dai abin da aka yi bayani kan haramcinsa. Wannan ka’ida ce da aka tabbatar da ita a kur’ani da hadisan Manzo (s.a.w) Saboda haka duk sa’adda babu wani dalili kan haramcin kayyade iyali ko tsara su ta daya daga wadannan hanyoyi to ya halatta a aiwatar da ita. Allah yasa mu dace!

 

 

What's On Your Mind?