NANS Ta  Kasa Ta Karrama Hajiya Aisha Maikurata A Kebbi

0
149

Uwar Kungiyar daliban kasar Nijeriya ta karrama Hajiya Aisha Muhammad Maikurata Babbar Sakatariyar a Ma’aikatar kula da harakokin mata a jihar kebbi a jiya a Birnin-Kebbi.

An gudanar da taron bikin karramawar a dakin gudanar da taro na Ma’aikatar kula da harakokin mata da ke a Birnin-Kebbi a jiya.  Inda jami’in yada labaru na uwar Kungiyar ta daliban kasar nan, kwamared Aminu Sani ya ce” kungiyar ta lura da irin ayyukkan na sadaukar da kai da Babbar Sakatariyar keyi musamman wurin inganta rayuwar matasa maza da mata na duk jahohin da kuma wasu na wajen jahar ta hanyar basu tallafin karatu da kuma koyar dasu sana’o’i hannu na zamani domin samu su iya dogaro da kai wurin gudanar da rayuwarsu a cikin al’ummar, inji kwamared Aminu Sani jami’in yada labaru na uwar kungiyar daliban kasar Nijeriya”.

NANS Ta  Kasa Ta Karrama Hajiya Aisha Maikurata A Kebbi

Ya ci gaba da bayyana cewar” a wani lokaci Babbar Sakatariyar Hajiya Aisha Muhammad Maikurata na daya daga cikin manyan mata a wannan yankin na jahohin Arewa maso Yamma da ke sadaukar da kanta wurin ganin ta tallafawa masara karfi ga tafiyar da rayuwarsu, inji shi”.

Saboda hakan ne muka yanke sharawar karrama Hajiya Aisha Muhammad Maikurata Babbar Sakatariyar a Ma’aikatar kula da harakokin mata a jihar kebbi domin karama ta gwarin gwiwa kan irin ayyukkan sadaukar da kai na alhairi ga al’ummar jihar da ma na wajen jahar. Bisa ga wannan aikin tallafi da take yi ne muka karramata .

Kungiyar Lauyoyi A Bauchi Ta Bukaci Gaggauta Wanzar Da Shari’o’i

A nata jawabin, Hajiya Aisha Muhammad Maikurata ta fara da mika godiyarta ga Allah da kuma shuwugabannin uwar Kungiyar daliban kasar Nijeriya kan ganin cewar irin ayyukkan da take yi ta chachaci yabo da karramawa, saboda hakan ta kara da bada tabbacin ci gaba da bada gudunmuwar ta ga mabukata da kuma masara galihu da sauran ire-iren su.

Daga karshe ta yabawa shuwugabannin uwar Kungiyar daliban kasar Nijeriya kan tunaninsu na bada lamba girma ta hanyar karramata kan ayyukkan sadaukar da kai da nake yi ga matasan jihar da ma na wajen jahar. Taron bikin ya samu halartar Daraktocin Ma’aikatar da sauran na wasu ma’aikatun gwamnatin jihar da kuma masoya da abokan arziki da sauransu.

What's On Your Mind?