NAF Ta Kai Ziyarar Ta’aziya Ga Dangin Marigayi Air Marshal Nsikak Eduok

0
77

NAF Ta Kai Ziyarar Ta’aziya Ga Dangin Marigayi Air Marshal Nsikak Eduok

Shugaban hafsan sojin sama (CAS), Air Marshal Sadikue Abubakar, a ranar, 9 ga Janairu 2021, ne ya kai ziyarar ta’aziyya ga dangin marigayi Air Marshal Nsikak-Abasi Essien Eduok. Marigayi babban jami’in wanda ya mutu a ranar 6 ga Janairun 2021, a wani asibiti da ke Uyo, Jihar Akwa-Ibom inda yake karbar magani, shi ne Shugaban sojin sama na 12 a tarihin Nijeriya.

Wannan sanarwar ta fito ne daga hannun Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar, Air Bice Marshal Ibikunle Daramola, a inda yake cewa, Air Marshal Abubakar, wanda matar mamacin, Uduak Nsikak Eduok ta tarbe shi, ya yaba da kyawawan halaye na marigayi tsohon CAS din, inda ya bayyana cewa, shi janar ne na kwarai da ya ba da gudummawa sosai ga ci gaban rundunar Sojan Saman Nijeriya (NAF). Shugaban ya kuma kai ziyarar ta’aziya zuwa gidan gwamnatin Akwa Ibom don jajantawa ga Gwamnan Jihar, Mista Udom Emmanuel, sport da rasuwar Air Marshal din, wanda shi ma tsohon Ministan jirgin sama ne.

Da yake magana yayin ziyarar a gidan Gwamnati, Air Marshal Abubakar ya nuna bakin cikinsa sport da rasuwar marigayi Air Marshal Nsikak Eduok. Ya jajanta wa Gwamnan da mutanen kirki na Jihar Akwa Ibom kan rashin tsohon CAS din, wanda, a cewarsa, babban gwarzo ne matukin jirgin sama kuma wani lokaci yana Jagorar ma’aikata a matsayin kwamandan sojoji na kwalejin jami’ai, Jaji.

Air Marshal Abubakar ya bayyana cewa, ko da ya yi ritaya, marigayi tsohon CAS din ya ci gaba da bayar da gudummawa mai matukar muhimmanci ga ci gaban hukumar, tare da muhimman bayanai kan yadda za a sake fasalta rundunar sojin don ganin ta yi tasiri sosai wajen tunkarar kalubalen tsaro na zamani da kasar ke fuskanta.

Ya ce, “Yanzu haka na kai ziyarar ta’aziyya ga dangin inda na tabbatar musu cewa NAF za ta kasance tare da su a shirye-shiryen binne shi kuma za mu hada kai da dangin don tabbatar da cewa an ba wannan babban dan Nijeriyar yadda ya dace. Wannan shine dalilin da ya sa muke nan da safiyar yau, kuma ina so in yi muku godiya sosai da gaske saboda duk goyon bayan da kuka ba wa dangi da kuma shi yayin da yake rashin lafiya. Amma rayuwa tana hannun Allah Madaukakin sarki. Wannan rashi ne na kowa, danginsa da kuma dukkanmu”.

Budurwa ta rasu kwanaki biyar kafin daura mata aure

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Mista Udom Emmanuel, ya gode wa shugaban sojin a kan gaggawar da ya yi sport da mummunan halin da jihar ta fuskanta, ta hanyar jagorantar wata tawaga ta Janarori da hafsoshi zuwa jihar a ziyarar ta’aziyya. A cewar Gwamnan, karimcin na nuna kyakkyawar zuciya da kuma nuna damuwar wadanda suka mutu. Gwamnan ya ce, a irin wannan mawuyacin lokacin ne mutum ya kan san su waye abokan sa na gaskiya. Ya tabbatar wa da shugabn sojin cewa ziyarar tasa ta yi tasiri wajen inganta alakarsu.

Da yake ci gaba da magana, Gwamnan ya bayyana cewa, kalubalen tare da marigayi tsohon CAS din na lafiyar ya fara kimanin shekaru 2 zuwa 3 da suka gabata kuma duk abin da aka yi don a raye shi, amma nufin Madaukaki ya yi nasara. Ya ce, “Babban bala’i ne kuma babbar asara ce ga jihar, musamman idan ya zama dole mu rasa manyan hafsoshin sojin sama biyu a cikin makonni 2, dayan kuma shi ne Shugaban Asalin Sojin wannan Jiha, Air Commodore Idongesit Nkanga (mai ritaya), wanda ya shude a ranar jajibirin Kirsimeti. Muna ta yi masa ta’aziyya ne kawai sannan kuma wannan babban mutumin, mai ba da shawara ga wannan gwamnatin, Air Marshal Eduok, shi ma ya wuce. Don haka kuna iya tunanin yadda muke ji, Allah ne kawai yasan yadda muke ji”.

Shugaban ya kasance a ziyarar ta’aziyyar da Shugaban Akawu da Kasafin Kudi na NAF, Air Vice Marshal (ABM) Clement Ogbeche, Shugaban horarwa da ayyuka, ABM James Gwani, Shugaban ma’aikata, Kwamitin Motsi, ABM HB Abubakar, da sauran manyan hafsoshin sojin.

What's On Your Mind?