NACOTAN Ta Gurfanar Da Sama Da Manoman Auduga Dubu Biyu A Kotu A Neja

0
89

NACOTAN Ta Gurfanar Da Sama Da Manoman Auduga Dubu Biyu A Kotu A Neja

Daga Muhammad Awwal Umar,

Kungiyar manoman auduga ta kasa reshen jihar Neja ta gurfanar da wasu manoman auduga kan zamba cikin aminci. Sakataren kungiyar Dakta ( Amb) Nura Hashim ne ya bayyana hakan ga manema labarai lokacin da yake karin haske kan sabon tsarin bada tallafi da kungiyar ta kasa ta fitar.

Daktan ya cigaba da cewar a shekarar da ta gabata mun samu matsala da wadanda mu ka baiwa tallafin, domin abinda mu ka yi tsammanin samu ba mu samu ba. Yankin Neja ta kudu mun rabawa manoman irin auduga amma sakamakon fari da aka samu mun samu hasara dan da yawa ba su noma ba, a yankin Neja ta tsakiya da Neja ta arewa an samu matsalar mahara ga manoma wanda wasu yankunan an hana manoman zuwa gona har zuwa lokacin girbi, wasu an hana su, wasu kuma maharan solar ce sai solar biya kudade kafin su tafi gonakinsu.

To wadannan matsalolin da dama yasa mun yi hasara, ba yadda mu ka za ta ba dan ba mu samu abinda muke so ba gaskiya, saboda wadannan matsalolin.

Mun yi hasara mai dama dan mun baiwa manoma kusan dubu hudu kayayyakin, kamar yankin Neja ta kudu, ita uwar kungiya ta nemi kayan da aka bayar, sauran kayyakin na hannun manoma. Bincike da mu ka gudanar a yankin sai mu ka fahimci solar yi anfani da kayyakin nan wajen wasu anfanin gonar na daban ba auduga ba, wasu kuma solar sayar, ita uwar kungiya da CBN suka ce ba ruwansu da hasara dole mutanan su dawo da kayan nan ko su biya.

Yanzu maganar da ni ke yi da ku mun kai manoman nan kotu dan su dawo da kayan ko su biya. Abinda aka yi shugabannin kungiyoyin da suka jagoranci karban kayayyakin da kungiyoyin su ne aka kai kotu, maganar gaskiya dai wadanda aka kai kotu yanzu solar fi dubu biyu.

Yanzu sabon tsarin da aka bullo da shi, shi ne uwar kungiya ta kasa ta soke baiwa manoma daidai tallafin na bashi, domin tace inda kungiya da jama’a da dama suka hadu wuri daya ne aka baiwa bashin, da aka samu matsalar bashi zasu ajiye kayan ne dan tunkarar wannan shekarar, abinda kawai zasu nemi a ba su sabon iri.

Shi yasa wannan shekarar suka ce sai kungiya ta kai mutum hamsin kuma ya zama wajen noman nan waje daya ba daban daban ba, idan manoman suka amince zasu yi noman na hadin guiwa suka aiko sai a tafi a duba yanayin wajen aka amince sai su shiga cikin sabon tsarin.

Yanzu mun samu manoma kusan dubu bakwai da suka amince da wannan sabon tsarin da muke kyautata zaton idan Allah ya taimaka zuwa wata mai fita za a na su kayan aikin. Wanda bayan wadannan kuma akwai wasu da suka nuna bukatarsu da yanzu haka muna tantance su da zaran mun kammala tantancewar su ma za mu tura sunayen su.

Bayan wannan kuma ganin wasu yankunan har yanzu akwai matsalar tsaro, ita uwar kungiya ta umurci a dakatar da manoman yankunan kamar karamar hukumar Mashegu, Mariga da Rafi. Sauran solar hada da Shiroro da Munya, yanzu haka dai ina kyautata zaton kananan hukumomi goma sha biyar solar tsallake wannan siradin cikin ashirin da biyar duk da cewar muna kan nazarin kara wasu kananan hukumomin da zasu samu shiga abin zai kasance bisa rahoton jami’an tsaro. Neja ta kudu dai ba su da matsala, ita ma Neja ta arewa wasu wuraren da sauki inda abin yafi kamari dai Neja ta tsakiya ce.

Tsarin bai canja ba, idan mu ka baiwa manoma kayan aikin idan lokaci yayi za mu bi su mu saye anfanin gonar a hannun su, sai dai abinda aka bullo da shi yanzu dan ana son sanya manoman cikin kungiya na din din din yanzu sai mutum yayi rajista zai biya dubu biyar sai mu tura sunan shi can wajen uwar kungiya ayi mashi katin zama dan kungiyar manoman auduga ta kasa wanda duk abinda ya taso da su za a cigaba da yi wanda ya kunshi cikakken bayanin mutum da wajen zaman sa kamar yadda aka bullo da tsarin a yanzu wanda kuma mutane na tururuwan yin wannan rajistan.

What's On Your Mind?