Na zo Najeriya bani da ko dinare ɗaya amma yanzu ni multi- biloniya ce- In Hadiza Gabon

- Advertisement -

Hadiza Aliyu Gabon yar shekara 32 a duniya. An haifeta a ranar 19 ga watan June 1989 a Libreville babban birnin Gabos. Ta yi karantun Diploma a harshe faransanci a Higher Institution based a Gabon.

Kamar yadda jaridar Mikiya na ruwaito.Bayan ta karɓi takardar diploma a shekarar 2006. Ta yanke shawarar zuwa Najeriya jihar Kaduna a shekarar 2007 domin ta cigaba da karatu, ta zauna a gidan wata yayarta da ta ke aure. Bayan wani loƙaci sai ta ji tana sha’awar shiga shirin fina-finai saidai a wancan loƙacin bata jin Hausa ko turanci

Daga baya, ta yanke shawarar tunkarar sarkin kannywood Ali Nuhu domin ya taimaka mata shiga harkar fina-finai a masa’antar Kannywood. Daga nan ne ta fara jan zaranta a fina-finan Hausa.

Yanzu haka Hadiza Gabon tana ɗaya daga cikin manyan jarumai a masa’antar kannywood sannan tana sahun waɗanda su ka mallaki biliyoyin daloli ta sanadiyar film

- Advertisement -