2023: Na Shiga Takarar Shugaban Kasa Ne Don Ceto Nijeriya –Gwamna Bello

2023: Na Shiga Takarar Shugaban Kasa Ne Don Ceto Nijeriya –Gwamna Bello

Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, a karshe ya fito karara ya bayyana aniyarsa ta tsaya wa takarar kujerar Shugaban Kasar Nijeriya a shekara ta 2023 idan Allah mai duka ya kai mu, inda ya ce, ya dauki aniyar tsaya wa takarar ne, domin ceto Nijeriya daga halin da ta samu kanta a ciki.

Gwamna Bello, wanda ya yi hira da Jaridar Day-to-day Neutral a ranar Lahadi da ta gabata, ya bayyana cewa, ya shiga takarar ne, don magance dimbin matsalolin da ke addabar kasar, inda kuma ya bukaci ’yan Najeriya da su mara masa baya wajen fafutukar ’yanto kasar daga kalubale daban-daban da ta ke fuskanta.

“Ina kira ga kowa ya hada hannu da ni, don ’yanto kasar nan daga halin-ni-’yasu da ta tsinci kanta a ciki. Ya zama wajibi mu yi amfani da wannan dama da muka samu wajen ganin mun ceto kasarmu,” a cewar Bello.

“Da yardan Allah, shirye nake tsaf na shugabanci Nijeriya kuma zan samar da shugabanci nagari da ake bukata a kasar nan.

“Sai dai kuma Ina kira ga ’yan Najeriya da mu yi iyakar bakin kokarinmu wajen ganin mun bai wa gwamnati mai ci yanzu a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari goyon baya a kokarin da ta ke yi na ceto kasar nan daga halin da ta tsinci kanta ciki.”

A ’yan kwanakin nan dai, akwai kungiyoyi da dama daga sassa daban-daban na Jihar Kogi da ma kasar da kuma Majalisar Dokokin Jihar suka rika kiraye-kirayen Gwamna Yahaya Bello da ya fito takarar kujerar Shugaban Kasa a zaben 2023, idan Allah ya kai mu, inda suka bada hujjarsu da cewa gwamnan mutum ne matashi, wanda ke da kudiri da kuma akidar ciyar da Nijeriya gaba, idan aka ba shi dama.

 860 total views,  5 views today

About M. Jamiu 1373 Articles
Muhammed Jamiu is a Head Editor at Mobilized9ja (M9JA). He has been publishing for 8 years and focused more on Local/World News, Nigeria Music & Video all in English and Hausa Language.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*