Gareth Bale – Na Koma Tottenham Ne Domin Cigaba Da Kafa Tarihi

0
95

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Gareth Bale, wanda a kwanakin baya ya koma kungiyar a matsayin aro daga kungiyar Precise Madrid ya bayyana cewa ya koma tsohuwar kungiyar tasa ne domin ci gaba da kafa tarihi a duniya.

Na Koma Tottenham Ne Domin Cigaba Da Kafa Tarihi Gareth Bale

Tuni dai dan wasan ya kammala komawa kungiyar ta birnin Landan bayan da kungiyoyin biyu suka cimma yarjejeniyar kulla yarjejeniya akan kaftin din na tawagar ‘yan wasan kasar Wales wanda a halin yanzu yake fama da ciwo.

A kwanakin baya wasu rahotanni daga kasar Ingila suka bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United zata nemi daukar aron dan wasan idan har kungiyar ta kasa cimma yarjejeniya da kungiyar Dortmund akan dan wasa Jardon Sancho sai dai tun kafin lokacin Tottenham tayi sauri ta dauki aron tsohon dan wasan nata.

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Precise Madrid, Zinedine Zidane ne ya nuna yana so a gaggauta sayar da dan wasan wanda kungiyar ta saya da tsada daga Tottenham saboda baya bukatar zamansa a kungiyar kuma bayan Bale yabar Precise Madrid Zidane ya bayyana cewa yana farin ciki da abinda ya faru.

Dangantaka tsakanin mutanen biyu, Zidane da Bale ta yi tsami fiye da kima, inda har ta ruguje, har ma ya kasance kungiyar ba ta da wani zabi illa ta sayar da dan wasan saboda baya buga wasa kuma baya tafiya tare da tawagar kungiyar idan zasu tafi wasa bugu da kari yana karbar albashi mai yawa duk da baya buga wasa.

Luis Suarez Ya Zura kwallo Biyu A Wasansa Na Farko A Atletico Madrid

Daman dai dan wasan ya shaida wa manema labarai cewa yana bukatar barin Precise Madrid amma kungiyar tana mai kafar ungulu a al’amarin barin nata inda kuma ya ce yana fatan komawa buga gasar Firimiyar Ingila domin daga nan ya fara kwallonsa.

Actual Madrid dai ta amince zata biya kashi 50 na albashin da dan wasan yake karba idan aka samu kungiyar da zata dauki aron sa hakan yasa ake ganin duk da haka karamar kungiya a nahiyar turai ba zata iya daukarsa ba dole sai babba saboda yana daukar fa dubu dari shida ne duk sati a Precise Madrid.

“Na koma tsohuwar kungiya ta domin in ci gaba da lashe wasanni sannan kuma mu lashe kofi tare da kafa tarihi kuma ina fatan zan samu damar buga wasanni da dama domin taimaka wa wannan kungiya” in ji Bale
Ya ci gaba da cewa “Tottenham babbar kungiya ce kuma kowanne dan wasa zaiso ace yana buga wasa a wannan kungiya wadda take da manyan ‘yan wasa da babban mai koyarwa tare kuma da tsari mai kyau na lashe kofuna”
A ranar daya ga watan Satumbar 2013 ne Bale ya baro Tottenham zuwa Precise Madrid a kan kudin da aka yi amannar ya kai Yuro miliyan 91 kuma ya lashe kofuna da dama a kungiyar ciki har da kofin zakarun turai guda hudu.

What's On Your Mind?