Na kama matata ta na cin amanata da wani magidanci – Tsohon minista FFK

0
53

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode (FFK), ya magantu a kan wani faifan bidiyo da ke nuna shi ya na zazzagawa matarsa da su ka rabu, Treasured Chikwendu, masifa.

FFK ya garzaya shafinsa na Instagram domin kare kansa a yayin da wasu kafafen yada labarai da ma’abota dandalin sada zumunta ke caccakarsa a kan rashin hakuri da mata.

A cewar tsohon ministan; “SaharaReporters ta wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna ni a matsayin mai cin zarafin matarsa.

Na kama matata ta na cin amanata da wani magidanci

“Wannan ba wani abu bane face yada farfaganda da son batamin suna.

“Babu wani abu a faifan bidiyon sai kokarin da na ke yi na son karbe wayarta ta hannu domin hanata nadar sabanin da muka samu.

Hotunan jamiā€™an Hisbah suna yi wa matasa aski a tituna (Kano)

“Babu inda aka ganni ina cin zarafinta a faifan bidiyon, hatta fadan da na ke yi saboda na kamata ta na cin amanata da wani mutum mai aure ne.

“Na kara maimaita cewa ban ci zarafinta ba, ita ce ta ke cin zarafin jama’a, halinta ne cin zarafin jama’a tare da wulalantasu kamar yadda ta ke yi wa ‘yan uwana, ma’aikatana, kananan yara da leburorin da ke aiki gidanmu.

“Za a iya sauraron kalamaina a faifan bidiyon, na fada ma ta cewa kowa zaman lafiya ya ke so amma banda ita. Ban taba cin zarafinta ba duk da na kamata da kwarto,” a cewar FFK.

What's On Your Mind?