Aubameyang – Na Fi Son Arsenal A Kan Barcelona

0
25

Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, kuma jagoran kungiyar a dai-dai wannan lokacin, Pierre-Emerick Aubameyang ya bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta nemi ya koma kungiyar amma yaki amincewa saboda yana son ci gaba da zaman Arsenal.

Na Fi Son Arsenal A Kan Barcelona Aubameyang

A farkon wannan watan ne Aubameyang ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya a kungiyar ta Arsenal bayan daukar dogon lokaci ana ko kwanton ci gaba da zaman sa a kungiyar ta birnin Landan.

dan wasan mai shekaru 31 ya sanar da kulla sabuwar kwangilar ta bidiyon daya wallafa daga filin wasan Fly Emirates dake London wanda hakan ya saka magoya bayan kungiyar cikin shauki duba da irin yadda suka damu da dan wasan ya ci gaba da zaman kungiyar domin ganin kungiyar ta dawo layin manyan kungiyoyi.

kungiyoyi da dam photo voltaic nemi dan wasan domin ya koma sai dai sakamakon lashe gasar cin kofin kalubale na FA da kuma yadda kociyan kungiyar Mikel Arteta ya zauna da dan wasan yasa ya amince da zaman Arsenal din.

Karshen Guardiola Ne Ya Zo A Ingila – Gary Neville

“kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta kawo min tayi domin in koma amma ina sane nace ba zan koma ba saboda ina son kafa tarihi a wannan kungiya kuma Mikel Arteta ya gaya min irin tsare-tsarensa hakan yasa naga gwanda Arsenal akan Barcelona” in ji Arteta.

Ya ci gaba da cewa “Arsenal tana daya daga cikin manyan kungiyoyi a duniya saboda haka dole ne manyan ‘yan wasa su kasance tare da kungiyar kuma ina fatan zamu samu damar zuwa duk irin matakin da muke bukata”

Kociyan kungiyar Mikel Arteta ya dade yana fatan ranar da dan wasan zai sake sabuwar yarjejeniya saboda a cewa Arteta dan wasan yana daya daga cikin manyan ‘yan wasa a duniya kuma yana fatan gina kungiyar a karkashin Aubameyang din.

“Ya na da muhimmanci Pierre-Emerick ya zauna tare da mu saboda babban dan wasa ne sannan kuma duk kungiyar da take fatan samun nasara a duniya dole sai tana da manyan ‘yan wasa Kamar sa,” a cewar kocin Arsenal Mikel Arteta.

Ya ci gaba da cewa “Yanzu hankalin shugabanni da ‘yan wasa da masu koyar da shi kansa Aubameyang din ya kwanta kuma zamu fuskanci kakar wasan bana domin ganin mun samu abinda muke burin samu kuma ‘yan wasa na photo voltaic gama shiryawa”

Aubameyang ya jefa kwallaye biyu a wasan karshe na cin kofin FA da Arsenal ta lashe a karawar da suka yi da Chelsea nasarar da ta baiwa kungiyar damar shiga gasar Europa da zai gudana nan gaba.

dan wasan ya koma Arsenal ne daga kungiyar kwallon kafa ta Borrussia Dortmund a shekarar 2018 ya kuma lashe takalmin zinare a gasar shekarar 2018 zuwa 2019 saboda yawan kwallayen da ya ci.

Aubameyang ya ci kwallon da ta bai wa Arsenal nasara a karawarta da Fulham ranar Asabar, a wasansu na firimiya na farko na kakar wasa ta bana kazalika dan wasan na Gabon ya zura kwallo biyu a wasan karshe na gasar FA da suka fafata da Chelsea a watan Yuli, abin da ya bai wa Arsenal damar samun gurbi a gasar Europa ta kakar wasa mai zuwa.

A kakar da ta gabata, Aubameyang ya zo na biyu wajen jefa kwallaye a Firimiya sai dai kafin ya saka hannu akan sabuwar yarjejeniyar kungiyoyi da dama wadanda ba’a bayyana sunayen su photo voltaic bayyana aniyarsu ta daukarsa ciki har da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.

What's On Your Mind?