Na Fada Muku Ba Zan Kamu Ba Saboda Aikin Allah Nake Yi – Shekau

0
138


Babbar Magana Shugaban Kungiyar Jama’atu Ahlisunnah Lidda’awati Wal Jihad wacce aka fi sani da Boko Haram, ya yi ikirarin cewa sojoji ba zasu iya kamashi ba saboda aikin Allah yake yi kuma ‘Allah zai kare shi’.

Shekau ya bayyana hakan ne a cikin sabon faifan bidiyo mai tsawon minti talatin da ya fitar domin mayar da martani ga rundunar soji, bayan fitar da sabuwar kalanda mai ɗauke da hoton shi da sauran hotonan ‘ya’yan ƙungiyar da ake nema ruwa a Jallo.

A cikin faifan bidiyon, Shekau ya bayyana a zaune kewaye da wasu muridansa guda biyu a wani daki marar yalwar fili.

“Babu wanda zai iya kamani saboda aikin Allah nake yi. Shine zai kareni da sauran masu aiki irin nawa da ke neman kariyarsa. “Ina da tabbacin cewa Allah zai kare kwamandojina. Aikin Allah muke yi,” a cewar Shekau.

A ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamba, rundunar soji ta sanar da sabunta farautar Shekau da sauran manyan kwamandoji a kungiyar Boko Haram.

A cikin sabon faifan bidiyon, Shekau ya amsa tambayoyi, inda ya ci al washin cewa ko ya mutu yakin Boko Haram ba zai kare ba. “Kamani ko kasheni ba zai dakatar da aikin ba, addinin ba nawa bane, na Allah ne, ku daina samun rudani,” a cewarsa.

Kazalika, Shekau ya yi tir da wasu kwamandojinsa da suka mika wuya ga shirin gwamnati na karbar tuban wadanda suka ajiye makamansu. “Solar bar hanyar addini,” a cewar Shekau, yayin da yake magana a kan irin wadannan kwamandoji.

Kafin ya kalkale bidiyon, Shekau ya zolayi rundunar soji a kan yawan fadawa jama’a cewa ya mutu duk da yana raye. Kazalika, ya alakanta wahalar da ake ciki a Najeriya da yakar Boko Haram da ‘ya’yan ta da gwamnati ke yi.

What's On Your Mind?