(Hotuna) Mutum daya ya mutu sakamakon artabu da ‘yan sanda suka yi da ‘yan fashi

0
39
  • Jami’an ‘yan sanda solar yi musayar wuta da wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne a jijhar Anambra

  • Wadanda ake zargi ‘yan fashin ne solar tare wani mota ne suna cikin yi wa ‘yan cikin motar fashi amma aka sanar da ‘yan sanda suka iso wurin

  • Da isowarsu sai miyagun suka bude wuta hakan yasa suka fafata daga bisani ‘yan sandan suka kashe daya daga cikinsu

An kashe wani mutum guda sakamakon musayar wuta da ‘yan sanda suka yi da gungun wasu da ake zargin ‘yan fashi ne a Isiagu ring street da ke Awka, babban birnin jihar Anambra a ranar 9 ga watan Oktoba.

Sanarwar da kakakin ‘yan sandan jihar Haruna Mohammed ya fitar ta ce an dade da sanin cewa wadanda ake zargin ‘yan fashin ne suna adabar matafiya da ke bin hanyar.

Bidiyon ragargazar da dakarun soji suka yi wa ‘yan bindiga a Katsina

“A ranar 9/10/2020 misalin karfe 9 an sanar da mu cewa wasu da ake zargin yan fashi ne solar tare Isiagu Ring street da ke karamar hukumar Akwa South suna yi wa wasu mutum uku da ke cikin mota bakar Accura Legend mai lamba SMK878GL fashi da bindiga.

“Isar jami’an ‘yan sanda na SARS da ‘yan banga na garin sai wadanda ake zargin ‘yan fashin ne suka bude musu wuta suka yi watsi da fashin da suke yi.

Mutum daya ya mutu sakamakon artabu da 'yan sanda suka yi da 'yan fashi

“Yayin musayar wutan, an raunata daya daga cikin ‘yan tawagar an kuma kwato bindiga daya da torch mild da wayoyin salula uku a hannunsa da kudi. An garzaya da shi asibiti inda likita ya tabbatar ya mutu aka kai gawarsa dakin ajiye gawa.

Mutum daya ya mutu sakamakon artabu da 'yan sanda suka yi da 'yan fashi

“Yan sandan solar datse dajin solar kuma sake nasarar gano wani bindiga da harsashi hudu. Ana cigaba da kokarin kamo wadanda ake zargin da ke neman tserewa da ake ganin an raunata su da harsashin bindiga,” in ji sanarwar.

What's On Your Mind?