Musulmi Sun Gudanar Da Idin Karamar Sallah A Xinjiang

- Advertisement -

Musulmi Sun Gudanar Da Idin Karamar Sallah A Xinjiang

Daga CRI Hausa

Al’ummar musulmin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai dake arewa maso yammacin kasar Sin, solar bi sahun daukacin musulmin duniya, wajen gudanar da Idin karamar sallah a Alhamis din nan.

Bayan sallar Idin da aka gudanar da sanyin safiyar yau, wadda ke alamta kawo karshen ibadar Azumin watan Ramadan, musulmin yankin da suka kunshi kananan kabilu da dama, solar kuma gudanar da bukukuwan raye raye a wurare daban daban, ciki har da filin dake daura da masallacin Id Kah dake birnin Kashgar, da kuma babbar kasuwar kasa da kasa dake Urumqi.

Masu yawan bude ido da dama solar halarci bukukuwan kade kade da raye raye, da aka gudanar albarkacin wannan rana ta idin karamar sallah.

Mazauna yankunan jihar solar yi amfani da wannan lokaci, wajen saye sayen kayayyakin abinci da na kwalam, domin tabbatar da gudanar da biki mai armashi.
A yankunan Qinghai, da Gansu da Ningxia ma, musulmi mazauna wuraren solar bi sahun jimillar musulmin kasar Sin su kimanin miliyan 20, wajen gudanar da wannan muhimmin biki.(Saminu)

- Advertisement -