Musulmi Su Yi Amfani Da Kwanakin Ramadan Wajen Addu’o’i – Cikasoron Minna

0
87

Musulmi Su Yi Amfani Da Kwanakin Ramadan Wajen Addu’o’i – Cikasoron Minna

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

 

An yi kira ga al’ummonin musulmi wajen yawaita addu’o’i da yawaita karatun Al’kur’ani dan neman gafara da samun zaman lafiya a Neja da kasa baki daya. Alhaji Sulaiman Yahaya Babangida, Garkuwan Talban Minna kuma Cikasoron Minna.
Basaraken ya cigaba da cewar ko lokacin yakin Biyafura da aka yi a baya, magabata solar tabbatar da cewar yawaita addu’o’i solar tabbatar an samu nasara ne dan kusanci da a ka yi ga Allah. Saboda yanzu ma lokaci bai kure ba, komawar mu ga Allah itace kawai mafita a halin da muke ciki a kasar nan, ya kamata gwamnati ta umurci malamai su tashi tsaye wajen yin addu’o’i dan samun zaman lafiya a kasar nan.
Da ya juya kan halin da matasa ke ciki kuwa, basaraken ya nemi iyaye da su sanya ido sosai akan amanar da Allah ya ba su na kulawa da tarbiyar ‘yayansu, tarbiya bai tsaya kan ciyarwa da sutura ba kadai, akwai bukatar sanya idanu akan yadda yara ke tafiyar da lamurransu, abokan huldarsu da yanayin huldodin su da jama’a.
Sanya yaro a turbar ilimi da sana’a na daga cikin ginshikan ginin tarbiyar rayuwarsa, bai kyautu yadda iyaye ke barin yara kara zube ba, hakan ne ke jefa a halin da mafi yawa suka tsinci kan su a yau.
Cikasoron na Minna, yace maganar cewar ana samun hannun wasu batagari shugabanni da ke labewa da sunan masarauta a yin kutunguila ga rashin tsaron kasar nan, abin takaici ne da bakin ciki matuka gaya, domin suna labewa da sunan masarautu suna cutar da jama’a, wanda ya kamata duk wanda aka tabbatar da hannunsa a irin wannan dabi’ar bayan cire mai rawani a hukunta shi yadda zai zama darasi ga wasu.
Ni kaina ina rike da sarautu a manyan masarautun kasar nan solar kai goma, wajibi ne duk abinda zan yi in tabbatar na kare martabar masarautun nan a matsayina na wakilin su. Lokaci yayi da za a dawo akan tafarkin tsaron kasa irin na baya, ta hanyar karfafa guiwar masarautun da ke kusa da al’umma.
A baya muna da sarkin tasha duk bakon da ya shigo ya san da shigowarsa, a arewa muna da sarkin yarbawa, inyamurai da makamantan su kuma suna taka rawa a harkar tsaro sosai, sarakuna ba iyayen kasa a taruka ba ne, iyaye da ya kamata su amsa sunan su na iyaye wajen sanya ido da kulawa da tarbiyar jama’a.
Alhaji Sulaiman Babangida ya nemi gwamnati da ta kara kaimi da azama wajen ganin ta kawo karshen matsalar tsaron da muke fuskanta a kasar nan, bai yiwuwa abubuwa su cigaba da kasancewa haka sannan a yi tsammanin za a samu cigaban da ake bukata.
Yau halin da muke ciki a jihar nan da kasa baki daya kowani magidanci na bacci ne da ido daya saboda bai san abinda dare zai haifar ba.

What's On Your Mind?