Murar Tsuntsaye: Bauchi Ta Kashe Kaji Dubu Hamsin

- Advertisement -

Murar Tsuntsaye: Bauchi Ta Kashe Kaji Dubu Hamsin

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Sakamakon sake bullo cutar murar tsuntsaye a Jihar Bauchi, gwamnatin ta yi kira ga masu kiwon kaji da masu kasuwancin su, da masu ci, hadi da masu ta’ammali da koyayen kaji da su rika bibiyar ka’idojin yin hakan domin a gujewa cutar.

kananan hukumomi biyu na Bauchi mai gonaki hudu da Toro da take da gonaki biyar wadanda wannan cuta ta murar tsuntsaye ta afkama, wanda a tsakanin biyun aka samu ‘tsintsaye dubu 50, 000 da aka kashe su har lahira, kuma ranar Alhahis din nan ne da ta gabata aka kashe guda 27, 000 daga cikin su a garin Narabi dake cikin karamar hukumar Toro a jihar.

Kwamishinan aikin gona da raya karkara na jihar, Sama’ila Adamu Burga, wanda ya bayyana barkewar cutar ‘tsuntsayen a ofishin sa dake Bauchi ranar Jumu’a da ta gabata, ya kuma ce akwai a halin yanzu wasu jihohi guda shida ma na kasar nan da suke da wannan cuta ta munar tsuntsaye.

“Abin farin ciki ne a wannan lokaci, mafi yawa daga cikin manoman mu, musamman masu kiwon kaji da ma’aikatan su, jami’an ma’aikatar gona, da masu sayar da Kwai ko sayen naman kaji, dukkansu an tantance su daga wannan cuta, ta hanyar daukar jinin su da aikawa zuwa hukumar NCDC inda aka tabbatar ba su da cutar.”
Alhaji Sama’ila Burga sai ya jawo hankalin jama’a, musamman ma masu kiwon kaji bisa bukatar dake akwai na sanya ido akan gonakin su, tare da sayen iri daga wuraren da suka dace, domin gudun daukar kara da kiyashi.

Kamar yadda ya bayar da tabbaci, ma’aikatar sa tana da horarrun ma’aikata guda 130 wadanda suke karade dukkanin kananan hukumomi ashirin da ake da su a jihar, suna bibiyar masu kiwon kaji da daukacin jama’a domin magance koke-koken su dangane da kiwon kaji da makamantan tsuntsaye dake tattare dasu.

Ya kuma yi tuni da furuci da hukumar NCDC ta kasa ta yi a kwanakin baya na samun mutane guda bakwai da aka yi da cutar murar tsuntsaye a jihohin Kano da Filato da suke makwabtaka da jihar Bauchi, tare da bukatar a samu hadin kai yadda za a yaki wannan cuta, tare da yiwa mutane kanda-garkin ta, la’akari da munin cutar ga bil-adama.

Burga, wanda ya bayyana cutar murar tsuntsaye a matsayin wata mummunar cuta wacce ke yaduwa tsakanin dabba da mutum, yana mai nuni da cewar, cutar tana kawo tasgaro wa tattalin arzikin kasa ta hanyar raba mutane da ayyuka ko sana’o’i da suka dogara dasu na inganta rayuwa, kamar Sarkar dake tashi daga jikin dabba zuwa ga mutum.

Kwamishinan, wanda ya bayyana cewar, cutar ta murar tsutsaye wacce take iya harbin mutum, har ma ta hassada kisa ta fara fullowa kasar nan ne a shekara ta 2006 a gonar Sambawa dake cikin jihar Kaduna, wacce daga bisani ta yadu zuwa wasu jihohin kasa, ta sake fullowa a shekara ta 2007, da 2015, da 2017, da 2019, kana ta bullo a wannan shekara ta 2021.

Famasi Burga, ya kuma ji takaicin yadda cutar ke tafiya da dawowa cikin wadannan shekara, tare da dakiye hanyar cin abincin jama’a, yana mai bayar da tabbacin cewar, ma’aikatar sa tana aiki tukuru tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki, da zumma kore wannan cuta daga jihar Bauchi.

- Advertisement -