Muna Fuskantar Mafi Munin Lokaci Na Farashin Dabba—In Ji Wasu Mahauta

0
126

Muna Fuskantar Mafi Munin Lokaci Na Farashin Dabba—In Ji Wasu Mahauta

Daga Bello Hamza, Abuja

Mahauta a yankin Birnin tarayya Abuja solar koka a kan hauhawan farashin dabbobi da su ke yankawa inda su ka ce ya ninka har sau biyu idan a ka kamanta da lokaci irin haka a bara. Madawakin sarkin fawan Kubwa Abuja Alhaji Abubakar Galadima wanda ya bayyana korafin a yayin zantawa da jaridar Management A yau, ya ce a tarihi ba su taba ganin tashin fasrashi dabba irin ta bana ba. Ya ce sau tari za su yi tafiya zuwa kasuwannin dabbobi irin ta Maigatari da ke jihar Jigawa ko Maiduguri a jihar Borno, amma sai su dawo haka nan ba tare da biyan bukata ba.

Ya ce haka lamarin ya ke a farashin manyan mota da su ke dauko dabbobin irin su tirela, inda a bangaren ma farashi ya ninka, inji shi. Ya ce kamar shekara daya baya a na iya daukan shatar motar tirela daga wuraren a kan naira dubu dari biyu, amma a yanzu farashin ya nika zuwa naira dubu dari hudu inda su ke daukan kamar shanu 30 a cikin babbar motar guda. “A harkar mai sayan shanu babu banki saboda dan kauye da ya kai dabbarsa a ranar kasuwar garuruwansu, ruwan kudin kawai ya ke bukata don yin sayayyar bikin aure ko wata hidima, a ranar.

“Ba ka fara yi masa maganar turansfa na banki saboda bai ma san shi ba, idan kuma ka ce za ka dogara da banki a na iya fuskantar rashin layin sadarwa ko kuma ya kasance solar tashi aiki idan ma ranan aiki ne, sannan POS kuma ba ya tabuwa, inji shi. Alhaji Abubakar Galadima ya ce karin farashi da su ke yi don ganin solar fidda kudin sa, ya sa su na fuskantar karancin masu iya sayan nama lamarin da ya jawo karancin dabbobi da su ke iya yankawa a yini.

“Misali kamar a mahauta ta nan Garin Kubwa, a rana irin ta yau Asabar da mu ka fi samun kasuwa mu na yanka shanu kama daga 40 har zuwa 50. “Amma sai gashi a yau wadanda mu ka yanka ba su kai 15 ba. Alhaji Abubakar Galadima ya ta’allaka lamarin yankewa da tsadan dabbobin da matsalar tsaro da a ke fuskanta musamman a arewacin Najeriya, inda ya ce a ke kora dabbobi tare da wargaza kauyuka da ’yan fashin daji ke yi. “A baya kamar nan kusa jihar Neja manomi Dan kabilar Gbagy zai tirke dabba a cikin gidansa a matsayin ribar kafa, amma duk wannan bai yiwuwa a yanzu.

Shi ma da ya ke karin haske a kan lamarin, wani jagoran mahauta a kasuwar Alhaji Ibrahim Abdullahi Lokoja Barden Fawan Kubwa, ya ce lamarin ya sa matasansu na fuskantar karancin aikin yi a tsakanin yara mahauta da ke aikin fawa da sauran kanannan ayyuka a mahautar. “ka na iya ganewa idanunka duk ga matasan nan su na zaune babu aikin yi kuma a farkon yini irin haka, wannan ba karamar matsala ba ce. Ya bukaci gwamnati da ta taimakawa masu sana’ar aikin fawa da isah shen jari kamar yadda ya ce ta ke taimakawa sauran bangarori na sana’a da kasuwanci don sake sabon damara na fuskantar yanayin da ya ce su ke ciki, inda ya yi korafin cewa yawanci jarinsu ya karye. Ya kuma bukaci gwamnatoci a dukkan matakai da su samar da masalaha a kan matsalar ta tsaro.

 

What's On Your Mind?