Muna Da Kwarin Gwiwa A Wasa Na Biyu – Arteta

0
93

Muna Da Kwarin Gwiwa A Wasa Na Biyu – Arteta

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta, ya bayyana cewa kungiyarsa tana da damar doke kungiyar kwallon kafa ta Villareal a wasa na biyu da kungiyoyin zasu fafata a sati mai zuwa a Ingila.

A ranar Alhamis din knowledge gabata ne kungiyar kwallon kafa ta Villareal ta yi nasarar doke abokiyar hamayyar ta Arsenal da ci 2-1 a wasan farko zagaye daf da karshe a gasar cin kofin Europa League da suka fafata a Spaniya.

Minti biyar da fara wasan kungiyar Villareal ta ci kwallo ta hannun Manu Trigueros, sannan Raul Albiol ya kara ta biyu tun kafin su je hutun rabin lokaci sannan Arsenal ta karasa wasan da ‘yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Dani Ceballos jan kati.

Arsenal ta zare kwallo daya ta hannun dan wasan gaba, Nicolas Pepe da hakan ya kara mata karfin gwiwa cewar za ta iya kai wa wasan karshe a mako mai zuwa a Ingila sannan saura minti 10 a tashi daga wasan Etienne Capoue na Villareal ya karbi katin gargadi na biyu da hakan ya sa shima aka yi masa jan kati a fafatawar.

Mai tsaron ragar Arsenal, Bernd Leno ya yi kokari sosai, bayan da ya hana kwallo biyu shiga raga da hakan ya kara karfin gwiwar ‘yan wasan Arsenal kuma Wannan shi ne karon farko da kungiyoyin biyu suka kara a Europa League, wanda Villareal ta yi nasara.

Tun a baya solar fafata sau hudu a Champions League, inda Arsenal ta yi nasara a biyu da canjaras biyu, kuma Arsenal ba ta taba cin kungiyar Villareal ba Spaniya sai dai a ranar 6 ga watan Mayu Arsenal za ta karbi bakuncin Villareal a wasa na biyu, domin fitar da wadda za ta kai karawar karshe a gasar bana.

Arsenal wadda take ta 10 a teburin Premier da saura wasa biyar-biyar a karkare kakar bana tana fatan lashe kofin domin ta samu gurbin buga gasar Zakarun Turai ta badi cikin ruwan sanyi.

 

What's On Your Mind?