Muna Ci Gaba Da Binciken Ibrahimovic, Cewar UEFA

0
69

Muna Ci Gaba Da Binciken Ibrahimovic, Cewar UEFA

Hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar turai, UEFA, za ta ci gaba da bincike kan dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta AC Milan, Zlatan Ibrahimovic, a kan bayanan da ke nuna kawancensa da wani katafaren kamfanin caca da kuma gagarumin hannun jarin da ya ke da shi a kamfanin.

Zlatan, dan asalin kasar Sweden, wasu bayanai da jaridun kasarsa suka wallafa ne suka bankado zargin ya yinda Uefa ta sha alwashin gudanar da bincike tare da daukar matakin da ya kamata.

Karkashin dokokin Uefa dai haramtaccen lamari ne samun hannun dan wasa a harkokin da suka shafi caca ya yinda hukuncinsa ke kaiwa ga dakatarwa ta tsawon lokaci wanda hakan zai saka babu tabbas idan zai iya wakiltar kasar a gasar cin kofin nahiyar turai da za’a fara idan an karkare kakar wasa ta bana.

Sanarwar da Uefa ta fitar, ta sanar da kafa kwamiti na musamman domin binciken lamarin wanda kuma kamar yadda rahotanni suka bayyana tuni bincike yayi nisa domin ganin lamarin kafin ayi masa hukunci.

A makon jiya ne dai dan wasan  mai shekaru 39 a duniya ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyar kwalllon kafa ta AC Milan bayan zura kwallaye 17 cikin wasanni 25 a wannan kaka.

Haka zalika a baya-bayan nan ne, Zlatan ya koma fagen dokawa kasarsa ta Sweden wasa  bayan ritaya shekaru 5 baya kuma yana da niyyar wakiltar kasar a gasar cin kofin nahiyar turai.

What's On Your Mind?