Mun Yaba Da Aikin Gina Babban Asibitin Machina -Sarkin Machina

0
76

Mun Yaba Da Aikin Gina Babban Asibitin Machina -Sarkin Machina

Kasantuwar yadda ake ta fama da matsanancin rashin lafiya, babba da yaro. A garin Machina dake jihar Yobe, idan rashin lafiya ta tsananta, to fa dole sai dai a kai marar lafiya din garin Nguru, sakamakon rashin babban Asibiti (Widespread Hospital) a karamar hukumar Machina. A wannan karon, gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya amince da a gina babban Asibiti a cikin garin na Machina, domin saukaka jama’ar yankin.

Wakilinmu ya tattauna da Mai Martaba Sarkin Machina, Alhaji Bashir Bukar Machinama a kan ginin Asibitin, ga abin da yake cewa; “Alhamdulillah! Muna godiya ga Allah da ya nuna mana wannan lokaci na mayar da karamin Asibitin mu (Predominant Healthcare) zuwa babban Asibiti (Widespread Hospital) a nan cikin garin Machina. Mun dade muna fatan samun hakan. Muna godiya ga mai girma gwamna Alhaji Mai Mala Buni bisa ga yadda ya inganta mana wannan Asibiti”

Bidiyo: Tambayoyi Malam Zan Iya Sakin Mata kuma Na Auri Yayarta ko Kanwar mahaifiyarta

“A da sai dai a kai marasa lafiya Asibitin garin Nguru, amma ga shi yanzu ana gina mana, na mu na kanmu. Kuma wannan Asibiti ba al’ummar garin Machina kadai zai amfana ba, har da al’ummar jamhuriyar Nijar. A makon da ya gabata na fita zan yi tafiya, na ga yadda aikin ginin Asibitin ke tafiya, cikin mako uku, gini ya yi nisa, har an buga rafta. Lallai muna jinjina wa kamfanin da yake gudanar da wannan aiki, wato AUM Multi Hyperlink Constructing Co. Nig. Ltd, gaskiya wannan kamfanin suna aiki mai inganci. Mai gwamna ma da kansa zai yi farin ciki da yadda aikin ke tafiya” inji shi

What's On Your Mind?