Mun Tanadi Filaye Eka 2,000 Don Samar Da Gidaje A Jihohi 24― Gwamnatin Tarayya

- Advertisement -

Mun Tanadi Filaye Eka 2,000 Don Samar Da Gidaje A Jihohi 24― Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, ta ware sama da fili mai fadin eka 2,000 da za ta bai wa jihohi 24, domin gudanar da shirin samar da gidaje. Mashawarcin mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande shi ya bayyana hakan a ranar Lahadi. Haka kuma ya ce, jihohi 17 ne za a gudanar da shirin samar da wutar lantarki ta hanyar hasken rana karkashin shirin farfado da tattalin arziki. Ya kara da cewa, a yanzu haka an kammala yarjejeniya da manyan kamfanonin samar da siminti da ke cikin kasar nan da zai samar da siminti a kan naira 2600 duk guda daya, domin kaddamar da shirin samar da gidaje. Ya ce, bayan mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbaji ya gama tattaunawa da manyan kamfanonin siminti guda uku wanda suka hada da Dangote Cement da Bua Cement da Lafarge.

Osinbajo ya bayyana cewa, wannan gwamnati za ta ci gaba da mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi da inganta wutar lantarki da samar da gidajen zama ga ‘yan Nijeriya a karkashin shirin farfado da tattalin arziki. Da yake bayyana irin nasarorin da shirin ya samu, mataimakin shugaban kasa ya tabbatar da cewa, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da bakin kokarinta wajen samar wa ‘yan Nijeriya wutar lantarki da gidaje. Ya ce, shugaban hukumar bunkasa wutar lantarki a yankunan karkara, Ahmad Salihijo ya nuna cewa, tawagar samar da wutar lantarki ta hanyar hasken rana solar kammala wannan aiki a jihoji guda shida. A cewarsa, jihohin Akwa Ibom da Ekiti da Kano an zabe su a matsayin jihojin da za a dunga gudanar kasuwancin shirin samar da wutar lantarki. A yanzu haka dai an samu nasarar gudanar da kasuwancin wanda ya kai na naira biliyan 55 a farkon mutane miliyan biyu a Nijeriya da samar da dabban ayyukan yi.
Ya ce, “misali, shirin ya gudanar da kasuwanci da bankunan ‘yan kasuwa guda hudu wanda ya samar da ayyukan yi guda three,500 da hada wa mutum 100,000 wutar lantarki.

“A cewar shugaban hukumar, ana bin kamfanin Bleu Camel Vitality bashin naira biliyan uku tare da tsammanin samar da ayyukan yi guda 600. Haka ma kamfanin Sunking ana bin sa bashin naira biliyan uku da kuma tsammanin samar da ayyukan yi guda 1,500. Kamfanin Audno ana bin sa bashi biliyan uku da tsammanin samar da ayyukan yi guda 100, yayin da kamfanin Emerald Industrial Co ke neman kudin naira biliyan uku da samar da cibiyoyin wutar lantarki guda 100,000.

“Mun samu nasarar samun filaye da za mu gida gidaje. A yanzu haka muna da fili mai murabba’in girma 2156, wannan fili zai gina gidaje guda 65,000,” in ji shi.
Mataimakin shugaban kasa ya ci gaba da cewa, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da hada kai da gwamnatocin jihohi domin tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya solar amfana da shirin samar da gidaje.
A karkashin shirin samar da gidaje, gwamnatin tarayya tana shirin bai wa ‘yan Nijeriya miliyan 1.5 gidaje, wanda za su dunga biya a hankali har zuwa shekaru 15 ko kuma su amshi haya. Ana tsammanin samar da ayyukan yi guda 1.eight da samar wa iyalai miliyan 1.5 matsuguni a Nijeriya. farashin gidajen solar kasance naira miliyan biyu da miliyan hudu, wannan ya danganta ne da yawan dakunan. Akwai mai daki daya, akwai mai biyu, sannan akwai mai uku.

- Advertisement -