Mummunar gobara ta barke, gidaje 620 sun kone na ‘yan gudun hijira a Maiduguri

- Advertisement -

Wata mummunar gobara ta yi ajalin wani jariri a wani sansanin ‘yan gudun hijira dake wuraren titin Mafa a cikin Maiduguri jihar Borno a ranar Talata.

Ganau sun tabbatar da yadda lamarin ya faru da misalin 7:30am na safiya a wani bangare na sansanin amma an samu nasarar kashe gobarar cikin karamin lokaci.

A cewar ganau din: “Wata gobara ta barke da misalin 1pm kuma ta yi sanadiyyar kone tanti da dama dake sansanin.”

Wani jariri ya kone kurmus sannan wasu manya biyu sun kone kamar yadda ganau din ya tabbatar.

An gano cewa wurin kwanan mutane 620 ne ya kone sakamakon gobarar wacce ‘yan kwana-kwana suka taru suka kashe, jaridar The Punch ta wallafa.

Abin da ya sa na dawo tare da album biyu – Nura M Inuwa

Mukaddashin shugaban NEMA na mazabar arewa maso gabas din Maiduguri, Ishaya Chinoko, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce Wants Evaluation tare da BOSEMA da wasu gidauniyoyi na tallafa wa jama’a suna kokarin ganin sun gyara wurin da suka kone.

Mummunar gobara ta barke, gidaje 620 sun kone na 'yan gudun hijira a Maiduguri

“Kwanan nan za a samar da wadanda wurarensu suka kone matsuguni,” a cewarsa.

A gaba daya sansanin akwai mutane 14,250 ne suke zama daga kananun hukumomi 3, Dikwa, Mafa da kuma Bama, Kamar yadda shugaban yace.

A wani labari na daban, gwamnonin yankin arewa maso yamma a ranar Litinin sun sha alwashin yin amfani da duk wasu hanyoyin da za su iya wurin bai wa rayuka da kadarori kariya a yankin.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya tabbatar da hakan a Kaduna yayin wani taro da ofishin mai bai wa kasa shawara a fannin tsaro ya hada, Vanguard ta wallafa.

Masari wanda yayi jawabi a madadin dukkan takwarorinsa, ya ce tsaro a yankin ya tabarbare don haka dole ne gwamnonin su yi aiki tukuru wurin tabbatar da zaman lafiya.

- Advertisement -