Mummunan Hatsarin Mota Ya Ci Rayukan Mutum 20 A Bauchi

0
15

Mummunan Hatsarin Mota Ya Ci Rayukan Mutum 20 A Bauchi

i mummunar hatsari mota ya faru a Bauchi inda mutum 20 suka kone da har hakan ya jawo ba a iya gane fuskokinsu.

Bayan da wasu motoci guda biyu suka yi taho-mu-gama da junansu a kan babban hanyar Maiduguri zuwa Bauchi, nan take mutum 20 daga cikin 22 suka mutu, yayin da sauran biyun suka gamu da raunukan masu tsananin gaske.

An gano hatsarin wanda ya rutsa da motar Bas Hummer mallakin kamfanin sufuri ta jihar Borno wacce ta dauko fasinjoji 18 da nufin zuwa Maiduguri daga garin Jos inda suka kara da wata mota Golf wacce take tahowa daga karamar hukumar Misau zuwa cikin garin Bauchi dauke da fasinjoji hudu.

A lokacin da hatsarin ya faru wutar gobara ya tashi da motocin lamarin da ya kai ga kona fasinjojin da har ba a iya gano fuskokinsu kai tsaye, sai dai jami’an ‘yan kwana-kwana photo voltaic yi kokarin kashe wutar da har mata biyu daga cikin fasinjoji suka tsira da munanan raunukan a jikinsu.

Harin Gujba: Gwamna Buni Ya Yaba Yadda Sojoji Suka Fatattaki Boko Haram

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin’yan sanda jihar Bauchi, DSP Ahmed Wakil ya shaida cewar an kwashi gawarwakin mamatan zuwa dakin ajiye gawarwaki da ke asibitin koyarwa ta ATBUTH yayin da kuma mata biyu da suka tsira suke amsar kulawar likitoci a wannan asibitin.

Wakil wanda ya ce ba zai iya tabatar da menene musabbbin hatsarin ba zuwa yanzu, amma jami’ansu photo voltaic kai dauki cikin gaggawa bayan samun labarin aukuwar lamarin domin kai agaji ga wadanda lamarin ya shafa.

Zuwa aiko da rahoton ba mu samu wani cikakken bayani daga hukumar kiyaye haduta FRSC a jihar ba.

What's On Your Mind?