Mummunan hatsarin mota ta halaka rayuka 10, wasu 30 sun jikkata

0
64
  • Ana fargabar mutum 10 sun mutu, 30 sun jikkata sakamakon hatsarin da treloli biyu suka yi a Adamawa

  • Wasu treloli biyu da ke kokarin yi wa juna obatekin sun yi hatsari a Mayobelwa a jihar Adamawa

  • Hatsarin ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane 10 yayin da kimanin wasu mutum 30 sun samu raunuka daban-daban

  • Hukumar kiyayye haddura, FRSC, ta tabbatar da afkuwar hatsarin inda ta ce an kai gawarwawakin da wadanda suka jikkata zuwa asibiti

Ana fargabar a ƙalla mutum 10 ne suka mutu yayinda wasu 30 suka jikkata sakamakon hadarin wasu treloli biyu suka yi a Adamawa a ranar Asabar.

Wani ganau ya shaida wa wakilin Day by day Belief cewa trelolin suna tafiya ne kan titin Mayobelwa – Ganye a jihar Adamawa kuma suka yi karo sakamakon kwacewa ɗaya daga cikin direbobin da motar tayi.

Wasu mazauna ƙauyen sun ce sun ciro gawarwaki 10 da kuma wasu mutum 30 da suka samu rauni bayan tirelolin biyu da ke gudu sun yi karo.

Mummunan hatsarin mota ta halaka rayuka 10, wasu 30 sun jikkata

Jami’an hukumar FRSC a Mayobelwa sun tabbatar wa manema labarai afkuwar hatsarin da suka ce gudu fiye da kima ya janyo.

Sun ce an kai gawarwakin da wadanda suka samu rauni zuwa wani asibiti a Mayobelwa.

Bidiyon ragargazar da dakarun soji suka yi wa ‘yan bindiga a Katsina

“Mun ga tireloli biyu sun tabo da gudu suna tsere; suna kokarin shan gaban juna, yayin hakan ne mota ta kwace wa ɗaya daga cikin direbobin,” a cewar ganau ɗin.

“Mun gano mutane da dama cikin motoccin: wasu sun mutu nan take, wasu kuma sun karye a hannu da kafafuwansu.

“Daya daga cikin wadanda suka mutu har kansa ya rabu da jikinsa.”

A wani labarin daban, Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya, ALGON, ta tsige mataimakin ta na ƙasa Mohammed Aliyu Soba daga muƙaminsa.

Mr Soba shine shugaban ƙaramar hukumar Soba a jihar Kaduna kuma shugaban kungiyar reshen jihar. Mohammed Aliyu Soba.

What's On Your Mind?