Muhimmancin Tsabtar Muhalli Ga Mata Masu Juna Biyu- Na’izatu Ado

0
96

Muhimmancin Tsabtar Muhalli Ga Mata Masu Juna Biyu- Na’izatu Ado

Na’izatu Ma’aikaciya a fannin lafiya ta ba wa mata sharawa da su mayar da hankali kan tsatace muhallinsu musamman masu juna biyu inda ta bayyana muhimmancin hakan. Malama Na’zatu ta ba da wannan shawara yayin da take tattaunawa Filinmu na Iyayen Giji. Ga yadda hirar tasu ta kasance.

Da farko masu karatu zasu so so jin cikakken sunanki da sunan da aka fi saninki da shi.
Sunana Na’izatu Ado muhammad, wacce aka fi sani da maman Al’ameen.

Ko za ki ba wa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
An haife ni a garin Kano cikin karamar Hukumar Fagge, kuma a yanzu ina tare da fannin lafiya.

Me ya ja hankalinki kika zabi fannin lafiya?.
Na zabi fannin kiwon lafiya ne saboda sha’awa, domin rashin yawan mata a cikin aikin, na samu damar taimakawa mata ta bangarori da dama.

Wacce irin matsala ce a bangaren lafiya ta fi addabar mutane?
Matsalar da ta fi addabar mutane ita ce ‘Maleria’ wato zazzabin cizon sauro

Wadanne hanyoyi ya kamata mutane su rika bi don ganin solar kiyaye kansu daga kamuwa da wannan matsalar?
Na farko dai tsabtar muhalli, rigakafin mata masu ciki, kwana a gidan sauro, da kuma daina barin ruwa yana taru wa a cikin gida.

Wace irin gudummawa shugabani ya kamata su rika bayarwa don bunkasa lafiyar al’umma?.
Na farko wayar da kai ta kafofin yada labarai, sannan kuma a dauki ma’aikan lafiya, a kuma wadata su da isassun kayan aiki

Wace rawa jama’a za su taka don gina lafiyar al’umma?.
Da fari sai an kafa kungiyoyi na kiwon lafiya a matakai daban-daban, sannan a sa’ido ga kayan aikin da hukuma ta samar musu, agaza wa gwamnati ta inda ta gaza.

Wanne kira za ki yi ga iyaye mata wajen ganin solar kula da ‘ya’yansu gudun kamuwa da cututtukan zamani?.
daukar shawarwari na kariya da ma’aikantan lafiya suka ba su, ba da abinci mai gina jiki, shayar da nonon uwa zallah, sannan tabbatar da tsabtar jiki da ta muhalli.

Akwai mata da yawa masu sha’awar irin wannan aiki naki na bangaren lafiya, wacce irin shawara za ki ba su don ganin solar cimma burinsu?.
Daukar shawarwari na kariya da maaikantan lafiya suka basu, bada abinci mai gina jiki, shayar da nonon uwa zallah, sannan tabtar jiki da ta muhalli.

Za ki ga wasu mazan suna da matan da su kai karatu irin naki, amma kuma solar gagara barin su su yi aiki, wane irin kira za ki yi wajen ganin solar bar matansu ko ‘ya’yan su solar yi irin wannan aiki?.
Ina kira ga mazaje da su bar matansu su yi aiki, domin karancin mata da ake da su a fannin lafiya, saboda za ka samu a wasu wuraren da dama maza ne suke duba mata a maimakon a ce mata ne suke duba ‘yan uwansu mata, wanda ko a fannin ardini ya zama kamar larura ne.

Wanne irin kalubale kika taba fuskanta a bangaren aikinki?
kalubale da na taba fuskanta shi ne, haihuwa lokacin ina cikin karatu.

Menene burinki na gaba recreation da aikin ki?
Burina shi ne in cigaba da karatuna har zuwa mataki na karshe, sannan kuma in ga ina taimaka wa mata ta fannin kiwon lafiya.

Wanne irin kira za ki ga sauran ma’aikatan lafiya?.
Na farko su daraja jama’a masu zuwa neman lafiya gurinsu, kula da zuwa wajen aiki da tashi a kan lokaci, sannan da kula da sa kayan aikin jinya

Me za ki ce da Jaridar MOBILIZED9JA?.
muna godiya da irin wadannan tambayoyi da suke yi wa gwamnati da al’umma da kuma mata akan harkokin kiwon lafiya mai dorewa.

Muna godiya da bamu lokacin ki da kikai.

What's On Your Mind?