Muhimmancin Aurar Da ‘Yan Mata Lokacin Da Suka Bukata

0
42

Muhimmancin Aurar Da ‘Yan Mata Lokacin Da Suka Bukata

Lallai akwai babbar illa ga tarbiyyar yara mata lokacin da suka bukaci yin aure aka hana su. ‘Yan mata da yawa solar fada cikin gurbacewar tarbiyya lokacin da suka bukaci yin aure aka hana su. Wani lokaci yara mata kan bukaci yun aure, amma sai iyayensu su hana su, ko don saboda karatu ko kuma wanda suka kawo su iyayen ba sa son su, ko kuma saboda wadansu dalilai na su na daban, wanda yin hakan ba karamar raunata tarbiyyar yara mata ya ke yi ba.

Sakamakon hakan, sai ka ga solar fada shaye-shaye, karuwanci da sauran wasu
hanyoyi da ba su dace ba. Kamar wata yarinya da ta bukaci mahaifinta ya yi mata aure, kuma har ma ta kawo wanda ta ke so, amma mahaifin nan ya ki, daga karshe yarinyar ta rubuta masa wasika cewa, “Na tafi idan ka zo Allah ya yi mana shari’a.” Sai ta hau saman bene, ta fado ta mutu har lahira. Haka zalika, an wata yarinyar da ta samu mahaifinta ta bayyana masa cewa, ya yi mata aure ko kuma ta lalace ta bi duniya.
Idan za a samu irin wannan lamari, to ya kamata iyaye su tashi daga barcin da suke yi wajen aurar da ‘ya’yansu a lokacin da suka bukaci hakan, ko da kuwa mahaifin nan bai da kudin aurar da ‘yarsa.
Idan har aka kai ga irin wannan matakin, to ya kamata shi uban ya kira saurayin nata ya bincika ya ga idan har mutumin kirki ne, to sai ya zauna da shi ya bayayyana masa cewa, shi fa bai da kudi, ya kawo abin da ya sauwaka sai a daura musu aure, domin yin hakan shi ne mafita.
Lallai iyaye su sani cewa Allah zai tsai da su ya tambaye su hakkin ‘ya’yansu ranar alkiyama, su daina cutar da ‘ya’yansu wajen hana su aure lokacin da suke bukata,
domin ba su san yadda suke ji ba. Idan har ‘ya mace za ta iya tunkarar mahaifinta a kan ya yi mata aure, to lallai hakan yana nuni da tura ta kai bango. Kamata ya yi iyaye su rika jin tausayin ‘ya’yansu wajen tashin hankali da suke fuskanta lokacin da sha’awa ta similar. Ba dai-dai ba ne a ce, iyaye solar yi sanadiyyar lalacewar ‘ya’yansu wanda Allah dankasu amanarsu a hannunsu.
Daga karshe ina kira ga iyaye su rage son abin duniya, domin abin duniya yana karewa
ya mutum, ko kuma mutum ya tafi ya bar abin duniya. Nuna kwadayin a kan sai ‘ya’ya mata solar kammala karatun boko kifin aure, wannan ba dilili ba ne. A aurar da mace idan mijinta ya bari ta ci gaba da karatu, to sai ta ci gaba, idan kuma ya ki yarda, to sai a bar ta da wanda ta samu tare da rokon Allah ya sa masa albarka. Ina fatan iyaye za su amfana da wannan karamar shawara tawa da kuma yin amfani da ita na barin ‘ya’yansu su yi aure a lokacin da suke bukata.

What's On Your Mind?