Wasan sada zumunci: Muhimman ‘yan wasan Najeriya 4 sun kamu da cutar korona

0
41

Tremendous Eagles, kungiyarv kwallon kafa ta kasa, za ta buga muhimman wasannin sada zumunci guda biyu

  • Najeriya za ta fafata da kasar Algeria ranar Juma’a sannan ta fafata da kasar Tunisia a ranar Talata mai zuwa

  • Sai dai, sakamakon gwajin da aka sake yi wa ‘yan wasan Najeriya a yau, Alhamis, ya nuna cew hudu daga cikinsu sun kamu da korona

A yayin da kungiyar kwallon kafa ta kasa ‘Tremendous Eagles’ ke shirin wasan sada zumunci, ‘yan wasa hudu sun kamu da cutar korona.

Najeriya za ta buga wasan sada zumunci da kasar Algeria ranar Juma’a sannan ta buga da kasar Tunisia ranar Talata.

Ana ganin hakan zai shafi kwazon kungiyar Tremendous Eagles a wasannin da za ta buga.

Babban kociyan kungiyar Tremendous Eagles, Gernot Rohr, ya ce ‘yan wasan suna cikin yanayi mai kyau duk da ya ki bayyana sunansu.

Muhimman 'yan wasan Najeriya 4 sun kamu da cutar korona

Subhannallah Kalli Bidiyon Yadda Mummunan Bala’i Ya Faru Ga Iyali A Cikin Al’umma

“Ba zan bayyana sunayensu ba duk da suna cikin yanayi mai kyau,” a cewar Rohr.

An sake gwada ‘yan wasan ne da ranar yau, Alhamis, gabanin wasan da za su buga gobe, Juma’a.

A daren ranar Laraba ne Legit.ng Hausa ta wallafa cewa hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 155 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Laraba 7 ga watan Oktoba, shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta fitar, ta ce mutanen 155 sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Lagos-84

Rivers-31

Kaduna-12

Osun-10

FCT-7

Oyo-6

Ogun-3

Kwara-2

What's On Your Mind?