Muhammadu Sambo Wali Gidadawa (Bagimbane): Gwarzonmu Na Mako (1)

0
26

Takaitaccen Tarihin Muhammadu Sambo Wali Gidadawa (Bagimbane):

Malamin Makaranta
Masanin Tarihi
Marubuci Wakokin Hausa

Haifuwarsa Da Salsalarsa

An haifi Muhammadu Sambo Wali a cikin birnin Sakkwato ranar 7 ga watan Agusta, shekara ta 1937 miladiyya. Sunan mahaifinsa shi ne Malam Muhammadu Salisu. Mahaifiyarsa kuwa, sunanta Malama A’ishatu. Muhammadu Sambo Wali Bagimbane ne a wajen mahaifinsa.

Wannan ne ya haddasa yawan wasan barkwanci da yake yi da Arawan Kangiwa da Nijar, wanda har yanzu ana irin wannan wasan tsakanin Gimbanawa da Arawa.

A wajen mahaifiyarsa kuwa Bafulatani ne. Wannan ne ya ba shi damar yin wasa da Bare-bari. Muhammadu Sambo Wali ya rayu a gidan ilmi da aka san muhimmancin tarihi musamman na sanin nasaba da salsala. Saboda haka ne Muhammadu Sambo Wali ya san kakanninsa. Shi dai dan Muhammadu Salisu ne. Muhammadu Salisu dan Muhammadu. Muhammadu dan Malam Yahya. Malam Yahaya dan Malam Abdussalami Bagimbane (almajirin Shehu).

Shi kuwa Abdussalami dan Malam Ibrahim. Malam Ibrahim dan Malam Shahru. Malam Shahru dan Mamman Ali Mai Babban Burgami. Mamman Ali kuwa dan Malam Jabbo Mai Gidan Marannu. Salsalar Muhammadu Sambo Wali ta bangaren mahaifiyarsa kuwa, Bafulatani ne kamar yadda bayani ya gabata.

Muhammadu Sambo Wali Gidadawa (Bagimbane): Gwarzonmu Na Mako (1)

Sunan mahaifiyarsa A’ishatu diyar Marafan Wazirin Sakkwato da aka fi sani da Marafa Tsoho. Shi kuwa Marafa

Tsoho Dan Waziri Sambo (Ambo) Ne.

Waziri Sambo dan Dangaladima Ahmadu. Dangaladima Ahmadu dan Waziri Usman Gidado (almajirin Shehu) da Nana Asma’u ne. Waziri Gidado dan Lema. Ita kuma Nana Asma’u diyar Shehu Usman dan Fodiyo. Fodiyo dan Usmanu ne. Shi kuwa Usmanu da Salihu ne. Salihu ko dan Haruna ne. Haruna dan Muhammadu Gurdo ne. Muhammadu Gurdo dan Jabbo ne.

Jabbo kuma dan Sambo ne. Shi ko Sambo dan Buba Baba ne. Buba Baba dan Baba Masarana ne. Baba Masarana dan Ayyuba ne. Shi ko Ayyuba dan Musa Jakollo ne. Shi kuwa Musa Jakollo ya fito ne daga Futa-Toro. Karatunsa Aikin waka, wato rubuta ta ko kuma nazarinta, ba aiki ne na jahili ko wanda bai iya karatu da rubutu ba.

Matasan Arewa: Gaba Kura Baya Siyaki (II)

Wannan ya tabbatar muna da cewa, Muhammadu Sambo Wali ya yi karatu, wanda yake shi ne ginshikin ci gaban dan Adam. Malam Muhammadu Sambo Wali ya fara karatun allo ne ga mahaifinsa, kuma ya yi saukar Alkur’ani tun yana dan shekara goma shabiyar. Wannan ne ya ba shi damar iya karanta haruffan Larabci a saukake.

Bayan da ya yi saukar Alkur’ani, sai ya ci gaba da neman ilmin sani, wanda aka fi sani da karatun zaure. Ya karanta littattafan sani da dama da suka shafi ilmin fikihu da hadisi da tarihi da luggar Larabci a wajen malamai da dama. Daga cikin malamansa akwai Malam Yahya Nawawi, Alkalin Lardi da Malam Jodi da Waziri Maccido da Malam Maigandi Gidadawa da Malam Babi Unguwar Dutsin Assada da Malam Sagware na Unguwar Alkanci da Malam Shayau na garin Kuci da Malam Gargajo na garin Kisasare.

A kowane lokaci Muhammadu Sambo Wali yakan tuna ire-iren nasihohin da wadannan malamai suka yi masa. Kuma ya tabbatar da cewa, photo voltaic ba shi kyakkyawar tarbiyya. Allah ya saka musu da alheri, ya jikansu da rahama tasa.

Ta Fuskar Karatun Boko Kuwa

Ba a bar Muhammadu Sambo Wali a baya ba, duk da cewa, a wancan lokaci ana kyamar karatun boko, musamman a garin Sakkwato.

Muhammadu Sambo Wali ya yi karatun elementary (main) a makarantar ‘Waziri Ward’, a shekarar 1942 miladiyya. Bayan da ya kammala karatunsa na firamare, sai ya tafi makarantar koyon Larabci, wato ‘College for Arabic Analysis’ da ke Kano. Bayan da ya dawo daga Kano a shekarar 1960 miladiyya, sai ya zarce a makarantar fasaha, wato ‘College of Arts’ ta Sakkwato a shekarar 1962 zuwa 1965 miladiyya.

A nan ne ya sami takardar shaidar kammala karatu mai daraja ta uku (Grade III). Karatun da Muhammadu Sambo Wali ya yi, ya ba shi damar samun ilmi ta bangarori daban-daban, musamman a kan bangarorin da suka shafi addini da tarihi da kuma harsuna. Saboda Muhammadu Sambo Wali yakan iya magana da karatu da harsunan Hausa, Larabci da kuma Fulatanci.

Wannan ne ma ya ke ba shi damar karanta wakokin da ke cikin wadancan harsunan, da ma rubuta su. Haka kuma, yakan iya magana da harshen Ingilishi da kuma karanta shi. Amma bai yi zurfi a harshen ba sosai. Aikace-Aikacensa Na Hukuma Muhammadu Sambo Wali ya fara aiki a ‘Gobernment Craft College’ da ke Sakkwato, a ranar 15 ga watan Satumba, shekara ta 1959 miladiyya, a matsayin mai koyarwa. Ya yi aiki a wannan makaranta har zuwa 1962 miladiyya.

Daga nan kuma sai ya koma makarantar firamare ta Tsafe a 1965 miladiyya. Sai kuma aka sauya masa wurin aiki zuwa makarantar firamare ta Gidan Madi a 1967 miladiyya. A nan ya ci gaba da koyarwa a matsayin malamin Arbiyya har tsawon wata shida. Yana cikin aikinsa a Gidan Madi sai ‘Gobernment Craft College’ ta sake neman a dawo mata da shi. Tabbas, Bahaushe ya yi gaskiya da ya ce, “kowa ya tuna bara bai ji dadin bana ba”.

Don haka, a kan wannan bukatar ne aka mayar da Sambo Wali can ‘Gobernment Craft College’, inda ya ci gaba da aiki har zuwa shekarar 1968 miladiyya. A karshen shekarar 1968 aka sake yi wa Muhammadu Sambo Wali sauyin wurin aiki zuwa garin Bukkuyum a makarantar firamare ta Bukkuyum, inda ya ci gaba da aiki har zuwa shekarar 1970 miladiyya. Daga nan kuma aka tura shi zuwa Tambuwal a makarantar firamare ta garin Bashire a 1972 zuwa 1973. Sai kuma ya tafi garin Ganuwa ya ci gaba da aikin koyarwa daga 1973 zuwa 1975 miladiyya.

Ya koma wata makarantar firamare a garin Romo, inda ya yi wata uku yana koyarwa a can. Daga Romo sai ya dawo cikin garin Sakkwato ya fara koyarwa a makarantar ‘ya’yan sojoji ‘Navy Children College’, inda ya shekara daya a nan. Wato daga 1975 zuwa 1976.

Daga nan kuma aka kai shi makarantar firamare ta garin Maruda, ya ci gaba da koyarwa zuwa shekarar 1978 miladiyya. A cikin shekarar 1978 ne gwamnatin Tarayya ta neme shi da ya sauya aikinsa na malamin makaranta zuwa aikin jarida a sashen yada labarai na Tarayya da ke Sakkwato. Muhammadu Sambo Wali ya karbi kiran hukuma inda ya kama aiki da gidan rediyon Tarayya sashen jihar Sakkwato (Rima Radio), tun daga 1978 har zuwa 1985 miladiyya. Hausawa kan ce “na gari na kowa, mugu kuwa sai uwar da ta haife she”.

Irin hazaka da kwazon Muhammadu Sambo Wali ne ya sa shugaban Jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sakkwato (na wancan lokaci), Farfesa Mahadi Adamu Ingaski ya roke shi da ya zo Jami’ar ya yi musu aiki. Muhammadu Sambo Wali kuwa ya yarda, inda ya bar aikin jarida ya dawo wa tsohon aikinsa, wato koyarwa. Ya fara aiki da Jami’ar ne a 1985, a Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci ta Jami’ar har zuwa 1996 miladiyya. Daga wannan lokaci kuma, sai Muhammadu Sambo Wali ~ 5 ~ ajiye aikin gwamnati.

Sai dai kuma Gidan Rediyon Rima photo voltaic sake nemansa a kan ya rika yi musu aiki na wucen-gadi. Inda yake kama musu a wani shiri da suke yi na fadakarwa mai suna ‘Zauren Mai Anguwa’. Tun daga wancan lokaci (1996) har yanzu (2012) ana aiwatar da wannan shirin tare da Muhammadu Sambo Wali. Sannan kuma, akan kira shi ‘Malam Mai Kunkuwa’ a cikin wannan shirin. Muhammadu Sambo Wali ya yi zama wakilin hukuma da kungiyoyi da dama na ci gaban kasa da al’umma da kuma harshe.

Cigaba a makon gobe in sha Allahu.

What's On Your Mind?