Mu Za Mu Mamaye Gasar Seria A Nan Da Shekaru Masu Zuwa – Conte

0
76

Mu Za Mu Mamaye Gasar Seria A Nan Da Shekaru Masu Zuwa – Conte

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan, Antonio Conte, ya bayyana cewa nasarar lashe gasar Seria A da suka samu zata taimaka musu domin su ci gaba da mamaye gasar ta kasar Italiya nan da shekaru masu zuwa.

A ranar Laahdi kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta yi nasarar lashe gasar Serie A karo na farko tun daga shekarar 2010 sakamakon kunnen dokin da kungiyar Atalanta wadda ke bin ta a teburin gasar na Italia ta yi da kungiyar Sassuolo a yammacin ranar Lahadi.

Inter Milan, wadda ta doke kungiyar kwallon kafa ta Crotone a ranar Asabar ta haramtawa kungiyar Jubentus kare kamun da ta samu a shekarar da ta gabata da kuma lashe kofin a karo na 10 a jere.

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Jubentus, Andrea Agnelli ya aike da sakon taya murna ga takwaran sa na Inter Steben Zhang sakamakon wannan gagarumar nasarar da suka samu ta lashe gasar ta bana.

Daga cikin ‘Yan wasan da suka taka gagarumar rawa wajen nasarar kungiyar Inter Milan akwai dan wasan gaba Rumelu Lukaku mai shekaru 27 da aka sayo yuro miliyan 80 daga Manchester United wanda ya zirara kwallaye 27, sai Nicolo Barella mai shekaru 24.

Sauran solar hada da dan wasan baya, Acraf Hakimi da kungiyar ta saya daga Actual Madrid da dan wasa Matteo Darmian da Christian Eriksen da aka sayo daga Tottenham Hotspur da Manchester United.

What's On Your Mind?