CBN – Mu Na Samar Da Tsarin Yakar Koma-Bayan Tattalin Arziki

0
91

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele, ya bayyana cewa, CBN yana kokarin samar da tsare-tsaren kudade da zai yaki koma bayan tattalin arziki, wanda tuni bankin ya yi nisa a kan hakan. Emefiele ya bayyana cewa, wannan yana da matukar mahimmanci sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da ake samu da kuma magance koma bayan tattalin arziki. Ya kara da cewa, wannan yana daya daga cikin abubuwan da kwamitin tsara-tsaren kudade suka tattauna a makon da ta gabata.

Mu Na Samar Da Tsarin Yakar Koma-Bayan Tattalin Arziki CBN

Ya ce, “kwamitin ya bibiyi dukkan wani kalubalen da ake samu ya ga babu wani zabi face gudanar da tsare-tsaren kudade wajen yin amfani da aiwatar da kayayyakin da za su bunkasa kudade da kokarin kara bunkasa samar da kayayyaki wanda zai kawo karshen hauhawar farashin kayayyaki a cikin kasar nan.

“A halin yanzu dai, tuni shirin yayi nisa wajen samar da tsarin da zai yaki koma bayan tattalin arziki da bunkasa hanyoyin samun kudaden shiga da saukar da farashin danyan mai da kuma rage yawan basukan da kasar nan take fuskanta.

“Domin haka, tsarin zai samar da bunkasan ayyukan kudade da kuma farfado da tattalin ar zikin Nijeriya,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, ta hanyar samar da tsarin za a samu dai-daituwar farashin kayayyaki, domin wannan shi ne babban abin da tsarin ya mayar da hankali a kai da kuma bunkasa tattalin arziki kafin karshen wannan shekarar ta 2020.

CBN Zai Wanzar Da Tsarin Samar Da Kudaden Musaya Don Dakile Shigo Da Madara

A cewar Emefiele, an samu kankacewar tattalin arziki a wata biyun farkon wannan shekara, wannan ne ya sa aka dauki matakin tsarin da zai yaki koma bayan tattalin arziki kafin karshen wannan shekara. Ya ce, domin haka ne ya sa aka kafa kwamitin da zai gudanar da wannan tsari. Gwamnan CBN ya bayyana cewa, an dai samu wasu matsaloli ne sakamakon cire tallafin mai da kara kudin wutar lantarki, inda aka samu hauhawar farashin kayayyaki wanda ta kai ga daukan wannan maki domin magance koma bayan tattalin arziki.

A cewarsa, wannan ne babban dalili kafa tsarin da zai yaki koma bayan tattalin arziki, domin cimma muradun farfado da tattalin arziki da kuma magance hauhawar farashin kayayyaki a cikin kasar nan. Emefiele ya ce, sakamakon gyara matsalolin canjin kudade wanda yana cikin abubuwan da ke kayyade farashin mai da na wutar lantarki, wannan ne ya sa CBN ya dauki mataki dai-daita harkokin kasuwancin canjin kudade. Ya ci gaba da cewa, CBN ya samar da bangaren kudaden da zai magance matsalolin kankantar rarraba man fetur da na wutar lantarki da samar da abinci.

What's On Your Mind?