Mu Dage Da Addu’a Don Kasa Ta Gyaru – Bashir Opp

0
30

ALHAJI BASHIR DAKATA, da aka fi sani da OPP, ya na daya daga cikin makusanta zababben Sanatan Kano ta Tsakiya, Sardaunan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya tabo abubuwa masu muhimmanci a recreation da Arewa a zantawar da ya yi da wakilin 247BAMBAM A YAU, SANI TAHIR. A yi karatu lafiya:

Mu Dage Da Addu’a Don Kasa Ta Gyaru – Bashir Opp

Masu karatu za su so sanin suna da kuma takaitaccen tarihin rayuwarka?
To Alhamdulillah, sunana Aminu Bashir Dakata wanda aka fi sani (OPP), wannan suna tun ana kuruciya aka samin sakamakon mu’amala da ake yi. An Haife ni a Unguwar Dakata na girma a nan na taso na yi karatu a Dakata Explicit Major School. Daga nan kuma sai makarantar sakadare ta Kawaji, bayan nan sai Allah ya nu feni da zuwa Jami’ar Bayero inda na samu shaidar karatun Diploma a Social Protection and Administration, wannan shi ne takaitaccen tarihina

Yaushe ne a ka fara harkar siyasa?
A gaskiya siyasa ta zama jini da tsoka, tun da na taso na ga a gidan mu Mahifina yanayi, da na tarar da shi yanayin irin siyasar tun lokacin ina dan karami idan zai tafi taron siyasa ya kan rike hannuna mu tafi tare, a nan nake gani har na girma wanda har nake da sha’awar ita kanta siyasar. Amma na shiga na fara yin zabe siyasa tun daga 1998, na tsaya na zama (Agent), wanda na karbi sakamakon zabe na dan takarar shugaban karamar Hukuma, daga nan na yi takarar kansila, sannan har izuwa yanzu muna ciki ana ta fafatawa damu. Alhamdulillah, idan ka duba za ka ga ana ta gwagwarmaya kusan shekara Ashirin da biyu ko da uku kenan.

Bambancin Sarakunan Baya Da Na Yanzun – Daga ’Yar Shekara 123

An san ka a siyasar gidan Sardaunan Kano, mutane suna ta kuka kan cewar kusan shekara daya kenan da zabensa a matsayin Sanatan kano ta tsakiya na rashin ganin ayyukan Sanatan me za ka ce a kai?
To, Alhamdulillah shi al’amari irin wannan ba sabon abuba ne ka samu abokin hamayya da zai dinga fadar wadansu maganganu wadanda san ransa ne kawai. Magana ta gaskiya abin da na sani, Mai Girma Sardaunan Kano zababben Sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, a matsayinsa na Sanata tun da ake yin zama na Kwamitocin da aka saka shi a ciki bai taba fashin zama ba ko da sau daya, yana halarta, hasali ma shugaban majalisar Dattawa ya jawo Malam a jiki domin idan babu wadanda suka san al’amuran rayuwa saboda tafiyar da harkokin majalisar za ta gagare shi, wannan ya sa ya jonyo su Malam suka zama diga-digansa don gudanar da abubuwa su tafi yanda ya kamata. Kuma maganar wai a ce Malam babu abin da ya yi wannan magana ce kawai ake fada kowa ya san Malam ya yi (Emporwerment), wanda shi ne ginshiki na rayuwa ka taimaki dan’adam ka gina mutum. Wannan (Empowerment) din yayi shi kusan sau uku a Shekara daya da ya yi a matsayin Sanata. Baya da wannan, abin da ake bukatar dan majalisar Dattawa ya yi shi ne ka je kakawo kudire-kudire, wanda wannan kudire-kudiren ga sunan ana gani, duk wanda yake dan fansho ne a Nijeria in dai yana jin Rediyo kuma zai fadi gaskiya ya san irin kokari da hobbasar da Mai Girma Sardauna ya yi kan hakkin ‘yan fansho ya fita, kwanaki an zo an tantance Zone din Kano, da Zone din Sokoto, an je ana tantance kowanensu. Batun ayyuka kuma ai ba laifin dan Majalisa bane, aiki ne na Majalisar zartarwa, yana nan yana hada kai da ita gwamnatin tarayya duk abin da ya kamata a saka an saka lokaci zai yi da za mu fito mu gayawa mutane.

Me za ka ce a kan tafiyar gwamnatin Jihar Kano?
Alhamdulillah, babu abin da za mu ce sai dai kawai mu gode wa Allah a recreation da tafiyar gwamnatin jihar kano, sai san barka dalili kuwa ko babu komai kowa ya shigo cikin Jihar Kano ya san zai ga ta canja fuska, ba irin Kano da ya sani ba, a daba, kuma shi Mai Girma Gwamna bisa shawarwarin da yake bi na su iyayen gidanmu, irin su shi Sardaunan Kano, abin da ake so a gwamnati cigaba daga inda ka gaji mutum ka dora, to mai Girma Gwamna ya dora wanda ga aiki nan ta ko ina ana yi a Jihar Kano.

Mu kalli tafiyar Shugaban Tarayyar Nijeriya wanda ya na zango na biyu. Wane kira ka ke da shi?
Magana ta gaskiya shi Mai Girma Shugaban kasa ya na da kyakkyawan shiri ga ‘yan Nijeriya, to amma duk inda ka kai mutum tara ya ke bai cika goma ba, a kwai matsaloli da ake samu a gwamnati wanda gwamnati tana da fadi ka dora mutum akan mukami ya yi kaza shi kuma abin da yake aiwatarwa daban, to amma magana ta gaskiya ana ta yin kokari kamar shi wannan shiri na bunkasa rayuwar mutane, na Social Inbestment Programme da bayar da tallafi ana ta kokari, ga tallafin manoman, masara, ga tallafin manoman shinkafa, ga tallafin noma na Korona. Akwai tallafin abubuwa da yawan gaske kawai sakacin mu ne, na ‘yan Arewa, idan aka ce an dora abu a yanar gizo-gizo ba za mu je mu cike ba, sai mu dawo gurin me shayi mu yi ta korafi, to ina kira ga mutane duk abin da aka ce gwamnati ta yi a dinga cikewa saboda yawan mutanen da na duba ‘yan kudancin kasar nan photo voltaic fimu samun ribar gwamnati, don haka mutane su dinga shiga cikin abubuwan gwamnati tana da fadi, daga randa aka yi zabe gwamnati ta zama ta kowa ayyuka kuma ana nan ana ta yi musu. Muna kara kira ga gwamnati da ta kara taimakon ‘yan Arewa da mu da muke da alaka da ita ta jam’iyya.

Mene ne sakonka na karshe?
Mutane da su dage da addu’a, domin duk wani aiki da za a yi idan har ana bukatar samun nasara sai an yi addu’a, Allah ya saka da alkairi.

What's On Your Mind?