Moghalu Ya Taya Farfesa Obiozor Murnar Zama Shugaban Koli Ta Ohanaze

0
34

Moghalu Ya Taya Farfesa Obiozor Murnar Zama Shugaban Koli Ta Ohanaze

Tsohon dan takarar Shugaban Kasa kuma Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Farfesa Kingsley Moghalu ya aika da sakon taya murna ga sabon shugaban Koli ta Ohanaze.

Moghalu a wata takardar sanarwar manema labarai wacce ya fitar yau Litinin a Abuja, ya ambaci sabon shugaban koli ta Ohanaze, Farfesa George Obiozor a matsayin masani kuma nagartaccen mutumin da ya kafa tarihi a mabambantan fannoni.

An Yaba Wa TAJBank A Kokarinsa Na Bunkasa Bangaren Ilimi

Farfesa Moghalu wanda ke rike da sarautar Ifek’ego Nnewi ya ce: “Sabon Shugaban Koli ta Ohanaze, Farfesa Obiozor ya kasance mutum mai nagarta da kwarewa. Za a ga haka idan aka duba irin aiki tukurun da ya yi lokacin da yake Ambasadan Nijeriya a Amurka, Isra’ila da Cyprus. Haka kuma a lokacin da ya ke Darakta Janar na NIIA.

“Obiozor Farfesa ne da ke da kwarewa ta jagoranci, wanda ya san zamaninsa da mu’amala da mabambantan mutane. Da wannan ne muke fatan cewa zai ciyar da wannan kungiya ta Ibo gaba, har ya kai ga an samu hadin kai na baidaya.” inji shi.

What's On Your Mind?