Miyagun Hanyoyin Mu’amala A Dandalin Sada Zumunci (Social Media)

0
101

Miyagun Hanyoyin Mu’amala A Dandalin Sada Zumunci (Social Media)

Daga Bello Hamza

Ga wadanda suke bibiyar wannan shafi tun farkon samuwarsa a shekarar, na san ba za su manta kasidu na musamman da muka gabatar kan asali da samuwa da kuma fa’ida ko cutarwar da ke tattare da sabon tsarin gudanar da rayuwa da ke kan habaka a giza-gizan sadarwa na duniyar yau ba. Wannan sabon tsarin mu’amala kuwa shi ne samuwar “Dandalin Sada Zumunci” ko “Dandalin Abota”, wato: “Social Media” ke nan a harshen Turanci.

A karon farko mun gabatar da kasida ne kan Dandalin Fb, mai take: “Dandalin Fb a Mahangar Masana,” cikin shekarar 2010. Cikin jerin kasidun mun kebance wani bangare da muka yi wa take: “Manyan Badakala a Dandalin Fb.” Wannan bangare yana dauke ne da labarai masu tayar da hankali, na takaici kan irin sakaci da halin ko-in-kula da jama’a ke yi wajen aiwatar da sadarwa a dandalin Fb, wanda kuma hakan ya haifar da hasara ko salwantar dukiya ko mutunci a idon duniya. Kafin nan, naje rowa su matsaloli wajen guda 10 da ke tattare da dandalin fb.

A shekarar 2013, 1 ga watan Janairu idan ban mance ba, kungiyar Tsangiyar Alheri na matasan da ke dandalin Fb solar gayyace ni taron su na shekara da suka yi a Katsina, inda na gabatar da kasida mai shafuka 14 mai take: “Rayuwar Matasan mu a Dandalin Abota.”Dukkan wannan kokari da yunkuri ne wajen fadakar da mu baki daya, don samun tsarin mu’amala mai tsabta a wannan mahalli mai cike da hadari.

To amma duk da haka, har yanzu da sauran rina a kaba. Abin nufi shi ne, a kullum ana samun karuwar masu mu’amala a wannan dandali. Sannan a kullum hanyoyi da tsarin wannan mahalli na sauyawa ne. A duk sa’adda ka dauki gajeren lokaci ba ka hau ba, da zarar ka hau sai ka ga wani abu sabo. kari a kan haka, akwai da yawa cikin mutane masu mugun nufi, wadanda ke amfani da jahilcin jama’ar da ke wannan dandali a duniya baki daya (ba wai a kasar mu kadai ba), da kuma sarkakiyar da ke tattare da manhajojin da ke, don cutar da jama’a ta hanyoyi daban-daban. Wannan ya sa na ga dacewar sake fadakar da mu don kara bude mana idanunmu, kar mu zama cikin wadanda za a kai mu a baro.

Sannan, sabanin tsarin da na bi a baya, inda na takaitu ga dandalin Fb kadai, a wannan karon zan duba hadurran da ke tattare da galibin ire-iren wadannan shafuka ne – Fb, da Twitter, da Youtube, da Whatsapp da sauran makamantan su.

“Like” ko “Comply with”?
Babu abin da ya fi sauki ga mai mu’amala a dandalin Fb musamman ko Twitter, irin matsa alamar “Like” ko “Comply with.” Asali dai wadannan alamomi ko isharori an samar da su ne don saukake mu’amala da kuma saurin sadarwa a wadannan kafafe.

To amma, kamar yadda masu iya magana ke cewa, idan kida ya canza, dole ne rawa ta canza. Abin nufi shi ne, ba kowane sako ka gani a Fb za ka matsa “Like” ba, kamar yadda ba kowa mutum ko kamfani ka gani a Twitter kawai za ka latsa “Comply with” ba. Mece ce matsalar? Galibin shafukan kamfanoni da ke Fb ko Twitter ba hakikanin kamfanoni ba ne, shafuka ne na bogi; ba su da asali. Za a turo maka hoton wata haja mai kyau, ko wani rubutu mai kayatarwa, ko hoton wata mace, sambaleliya, abin sha’awa, duk na bogi ne.

Abin da ke faruwa shi ne, akwai mutane da yawa mazambata masu bude shafukan kamfanonin kasuwanci iri-iri, don tarajama a shafin, da niyyar “sayar” da su ga wasu kamfanoni don a ci gaba da tallata musu hajoji nau’uka daban-daban. Kana iya ganin shafi (Fb Web page) na kamfani dauke da “20,000 Likes” misali. Mai wannan shafin zai je ne kai tsaye ya sayar da wannan adadina likes ga wani kamfani da ke neman wadanda zai rika tallata hajojinsa garesu.

Iya yawan ku iya yawan kudin da zai samu. Watakila ka ce ai haja ce, ba matsala. In ji wa? Galibin kan sayar da wadannan bayanai ne shafukan batsa da ke Intanet. Kuma ka sani, iya yawan shafukan da ka “So” iya yawan wadanda za su iya isa ga profile dinka, don tattaro bayanan da suka shafeka.

Manhajar “Who views”
Daga cikin dodorido da badakalar da ke dandalin Fb da Twitter musamman, akwai wasu kananan manhajoji da ake yawo da su ko dai a Android Playstore, ko kuma dandalin Fb din, cikin tarkacen da ke yawo da sunan “Instructed Pages” ko “Instructed Apps.” Shahararriya daga cikin ire-iren wadannan manhajoji ita ce manhajar “Whobiews.” Meye aikinta?
Wannan manhaja ce da ita kan loda ta a wayarka ko kwamfutarka, nan take za a nuna maka masu alkaluma na bayanai da a cewar manhajar, wai yawan mutanen da suka kalli “Profile” dinka ne a Fb. Adadin lambobi za ka gani bai hakikanin sunayen su ba. Da yawa cikin mutane kan loda wannan manhaja don sanin yawan mutanen da suka kalli “Profile” dinsu. Sai dai kuma, bayan an nuna maka wannan adadi na wadanda aka ce solar kalli “Profile” dinka, yana da kyau ka san cewa wannan manhaja ce da ake amfani da ita wajen satar bayanai, daga wayarka har zuwa wadanda ke cikin kwamfutarka, idan a kanta ka loda. Ba ita kadai ba, galibin manhajojin da za ka ga suna shawagi da tutiyar za a nuna maka yawan abokanka, ko yawan wadanda suka ga profile dinka, ko yawan “Likes” din da kalatsa tun shigarka Fb, duk manhajoji ne ‘yan cuwa-cuwa. Suna yi maka kyauta ne ta hannun dama su kwace ta hannun hagu. Sai a kiyaye.

Bidiyo Mai Ban Al’ajabi
Abin da ya fi komai tasiri a zuciya da kwakwalwar da nadama shi ne abin da yake gani ana aikatawa a aikace, kuma yake sauraronsa duk a lokaci daya. Daga cikin nau’ukan bayanan da ke Intanet babu wanda ya hada wadannan siffofi sai “Bidiyo.” A bidiyo ne za ka ga rubutu, ka karanta. Za ka ga hoto mai motsi, ka kalla. Sannan za ka ji abin da ake fada a cikin hoto mai motsin, ka saurara. Idan aka yi rashin sa’a abin da ke bidiyon abu ne da kake so, kuma mummuna, to, kafin wani lokaci kwakwalwarka ta hadda ce shi, sannan zuciyarka ta nade.

Ga mutumin da ya saba hawa shafin Youtube na kamfanin Google, zai ba da labari. A shafinYoutube akwai nau’ukan bidiyo iri-iri; masu kyau da mummuna. Na Imani da na kafirci. Na tauhidi da na shirka. Sai wanda ka zaba.

Duk da cewa hukumar Youtube solar killace adadin shekaru ga wasu nau’ukan bidiyon, amma wannan bai hana komai, ga wanda ya san lamarin.

Youtube shafi ne kuma rigiza ce ta ilimi. Ba don kada in yi sabo ba, da sai in ce maka duk abin da kake nema na ilimi, za ka samu yadda ake koyonsa ko aikata shi a aikace. Iliminka da abin, da sanayyarka ga hanyoyin samunsa, da kuma imaninka ne kadai za su agaza maka.

Idan muka koma bangaren Fb, na tabbata da yawa cikin masu karatu solar ga sauyin nau’ukan bayanan da ake mu’amala da su a dandalin. Musamman daga shekarar 2014 zuwa yanzu. Akwai wasu nau’ukan bidiyo da za ka ga suna yawo, mutane suna yada su, daga wasu shafuka ne asalinsu. Da zarar ka kai hannunka kansu kawai za su fara nunawa kai tsaye.

Idan a kwamfuta kake, da zarar ka kai beran kwamfutarka (Mouse) saman hoton bidiyon kawai nan take zai fara nunawa.

Wadannan bidiyo galibinsu suna dauke da abubuwan al’ajabi ne na rayuwa. Asalinsu, kamar yadda na fada a farko, daga shafukan kasuwanci ne. Za ka ga an ce idan kana son karin wasu, ka matsa “Like” ga bidiyon. Idan ka yi haka, ka zama kwastoma karfi da yaji. Za su rika cillo maka wadannan hotunan bidiyo don tallata hajojinsu. Ka ga kai kana takamar ka samu abin kallo, kullum ana ja maka “Knowledge”, a daya bangaren kuma kana tallata musu hajarsu. Idan ba ka yi sa’a ba, wadannan hajoji nasu na iya zama na batsa ne.

What's On Your Mind?