Ministan Abuja Ya Bukaci A Cafke Da Gurfanar Da ’Yan Wawason Rumbuna

- Advertisement -

Ministan babban birnin tarayya Abuja (FCT) Malam Muhammad Bello ya bada umurnin a cafko tare da gurfanar da wadanda suka balle rumbun adana kayan abinci na FCT da ke yankin Gwagwalada tare da kwashen kayan abinci da ke ciki.

Minista Bello ya bada wannan umurnin ne a lokacin zaman gaggawa kan tsaro da suka gudanar da shugabannin bangarorin tsaro a cikin birnin Abuja jiya Litinin.

Ministan Abuja Ya Bukaci A Cafke Da Gurfanar Da ’Yan Wawason Rumbuna

Ministan ya nemi wadanda suka sanya hannunsu wajen sace kayan da su gaggauta maido da su wuraren da suka diba, ya kuma sanar da cewa an jibge jami’an tsaro a wuraren adana kayan abinci da suke birnin domin dakile yunkurin sake hakan a nan gaba.

“Wannan abun da ya faru ya tashi daga maganar zanga-zangar #EndSARS barayi ne kawai,”

#EndSARS: Etsu Nupe urges youths to be patient with Federal Government

A nata fannin, karamar ministan FCT Dr Ramatu Aliyu ta yi tir da sace kayayyakin, tana mai cewa babu wata kasa da za ta ci gaba ba tare da adana abinci a rumbunanta ba.

Ta nemi sarakuna da limamai da su dukufa bayyana wa jama’ansu illar sata.

Sarakunan da suka yi magana a wajen photo voltaic nuna rashin dacewar sace kayan, suna masu cewa hakan ba zai zama cigaba ga kasa ba.

- Advertisement -