Minista Ya Bukaci Kara Tsaurara Tsaro Don Kawo Karsshen Kai Farmaki Gidan Yari

0
101

Minista Ya Bukaci Kara Tsaurara Tsaro Don Kawo Karsshen Kai Farmaki Gidan Yari

Daga Maigari Abdulrahman,

Biyo bayan yawaitar farmaki a gidajen yari a fadin kasar, gwamnatin tarayya ta ba jami’an tsaro umurnin bindige duk wanda ya yi yunkurin kai farmaki, ko tayar da tarzoma a ciki.

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Aregbesola ne ya bayar da umurnin a wani zaman gaggawa da shugannin gidajen yari da na jami’an tsaro kan lamarin.

Ministan, ya nemi da su tabbatar da kariya ga gidajen yari a kowane irin hali, “Aikin ku ne kare gidajen yari, kuma kuna da bindiga da kayan aiki. Abinda ya hau kanku shi ne kariya ta kowane hali,” in ji shi.

“Bari na maimaita, ku kare su ko ta kowace hanya. Dokar kasa ta baku damar bada kariya. Makaman ku domin kariya ne, duk wanda ya yi yunkurin farmaki daga ciki ko waje, to ku dauke rayuwar sa,” in ji ministan

Ministan ya ja hankalinsu da cewa, “Dole ne ku bada kariya, rashin yin hakan zai zama gazawarku, kuma kun taimaka wa matsalar tsaron da ke addabar kasar ta barin bara gurbi aikata barna.

“Aikin farko shi ne sa ido. Dole ne ku zama ankare da duk abinda ke kai komo ciki da waje. A wannan watan ma, wani  mai’aikaci ya yi yunkurin shigar da wayar hannu ga fursuna a Bauchi, wasu ma’aikatan ne su ka hanshi hakan.”

Ministan ya kara da cewar, “Kafin furssuna ya iya samun damar yin wani abu, to sai da sa hannun wani jami’I ko ma’aikaci, ko yaya ne kuwa.”

“Kar a sake barin wani hari ko farmaki ya faru a gidajen yarinmu, kai ko ma a gonakinmu ne. Duk wanda ya yi yunkuri, to ba shi ba sai dai wani. Idan su ka fara ji a jikinsu, to za a samu zaman lafiya,” ministan ya karkare.

A nasa jawabin tun a farko, shugaban riko na hukumar gidan, Mista John Mrabure ya caji ma’aikata da su kara kaimi, ya kuma ce za a hukunta duk wanda aka samu da laifi a cikin su, haka kuma akwai la’ada ga masu kwazo.

 

What's On Your Mind?